An Fille Kan Sarki Yayin Rikicin Rabon Kudi A Jihar Delta

An Fille Kan Sarki Yayin Rikicin Rabon Kudi A Jihar Delta

  • Wasu bata gari sun fille kan Obi Okwudiki Odumodu, sarkin garin Asamokwu da ke jihar Delta a yankin kudu maso kudancin Najeriya
  • DSP Bright Edafe, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Delta ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa rikicin rabon kudin man fetur da kamfani ta bawa garuruwan ya janyo rikicin
  • Edafe ya ce wani kamfanin man fetur a yankin ne ya bawa garuruwan kudi don su raba amma aka kaure da rikici yayin rabon kudin

Jihar Delta - Rundunar yan sandan jihar Delta ta ce an halaka basaraken garin Asamokwu, Obi Okwudiki Odumodu.

An datse kansa yayin rikicin da ya biyo bayan fada da aka yi kan rabon kudin kason albarkatun man fetur.

Taswirar Delta
An Datse Kan Basaraken Jihar Delta Yayin Rikici Kan Rabon Kudin Man Fetur. Hoto: Mobile Punch
Asali: UGC

Kakakin yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe ya bayyana hakan a ranar Juma'a a Asaba, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Makarantun Adamawa, Borno, da Yobe Basu da ƙwararrun Malamai – UNICEF

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An datse kan Obi Odumodu a ranar Alhamis yayin rikicin da aka yi tsakanin garuruwa biyu a karamar hukumar Ndokwu ta Gabas na jihar Delta.

Punch Metro, a baya ta rahoto cewa wasu bata gari sun kashe basaraken kuma sun kashe sojoji hudu yayin wani hari da suka kai musu inda uku suka mutu nan take daya kuma ya karasa a asibiti.

Amma a wani sabon cigaba, kakakin yan sandan jihar ya ce:

"Rikici ne a tsakanin garuruwa. Sun jayayya ne kan kudi da suka fito daga kamfanonin man fetur da ke aiki a yankin.
"An kashe basaraken a lokacin da ake jayayya tsakanin garinsa da garin da ke makwabtaka kan raba kudin da kamfanin man fetur ta basu.
"Garuruwan suna rikici ne kan ribar kudin man fetur din. Bangarorin biyu suna rikici. Don haka, rikici ne tsakanin garuruwa."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hankula Sun Tashi Yayin Da Yan Bindiga Suka Kashe Sojoji 4 A Harin Kwanton Bauna A Delta

Edefe, ya ce ana kokarin tabbatar da zaman lafiya a garuruwan, ya kara da cewa an kama wadanda ake zargi.

Yadda yan ta'adda suka fille kan tsohon dan majalisa a jihar Anambra

A wani rahoton a baya kun ji cewa wasu bata gari sun halaka tsohon dan majalisa na jihar Anambra mai suna Nelson Achukwu.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana yan daban sun halaka Achukwu ne wanda ya wakilci yankin Nnewi ta kudu saboda zarginsa da kai wa sojoji tsegumi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164