Gwamnatin Kano Ta Maka Gwamnatin Tarayya A Kotu Kan Sauya Fasalin Naira, Ta Bada Dalili

Gwamnatin Kano Ta Maka Gwamnatin Tarayya A Kotu Kan Sauya Fasalin Naira, Ta Bada Dalili

  • Gwamnatin jihar Kano ta maka gwamnatin tarayya a kotu kan tsarin sauya fasalin takardun naira
  • A karar da ta shigar mai lamba SC/CS/200/2023, jihar ta bukaci kotun kolin ta ayyana cewa Shugaba Buhari shi kadai ba zai iya umurtar CBN ta canja kudi ba
  • Jihar ta kuma roki kotu ta hana gwamnatin tarayya da CBN karbe tsaffin takardun N200, N500, da N1000 daga hannun mutane a gari

Jihar Kano - Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta maka gwamnatin tarayya a kotun koli kan tsarin sauya fasalin naira na babban bankin Najeriya, CBN.

Antoni Janar na jihar Kano ta hannun lauyansa, Sanusi Musa, ya roki kotun kolin ta ayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari shi kadai ba zai iya umurtar CBN ta haramta amfani da tsaffin N200, N500 da N1000 ba a kara mai lamba SC/CS/200/2023, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ku Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudadenku, Zamu Bi Umurnin Kotun Koli: Gwamnatin Tarayya

Ganduje da Buhari
Gwamnatin Kano Ta Maka Gwamnatin Tarayya A Kotu Kan Sauya Fasalin Naira, Ta Bada Dalili. Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalilin da yasa gwamnatin Kano ta yi karar gwamnatinn tarayya a kotun koli

A karar, jihar tana bukatar kotun ta ayyana cewa akwai bukatar shugaban kasar ya tuntubi majalisar zartarwa na kasa da kwamitin tattalin arziki na kasa kafin daukan irin wannan matakin.

A cewar takardar karar da aka shigar, jihar na Kano na son kotun ta bada umurnin tilasta gwamnatin tarayya ta janye tsarin hana amfani da tsaffin N200, N500 da N1000 a kasar.

Ta ce tsarin na kawo matsala ga tattalin arziki da walwalar mutane fiye da miliyan 20 da ke zaune a jihar Kano.

Jihar ta Kano kuma tana son kotun kolin ta tilasta wa gwamnatin tarayya janye tsarin sauya fasalin nairan, tana mai cewa tsarin ya ci karo da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Kara karanta wannan

Bawa ba zai kamu ba: EFCC ta dauki mataki kan umarnin kotu na cewa a kama shugabanta

Canja Naira: Bola Tinubu ya yaba wa Matawalle, El-Rufa'i Be Bello Kan Yin Karar Buhari a Kotu

A wani rahoton na baya kun ji cewa dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progress Congress, APC, mai mulki a kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa gwamnoni da suka yi karar gwamnatin tarayya a kotu.

Gwamnonin jihar Kaduna, Zamfara da Kogi ne suka shigar da gwamnatin tarayya inda suka ce tsarin na barazana ga tattalin arziki da walwalar mutanen kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164