Dakarun Sojoji Sun Halaka Ƴan Ta'adda 77 a Arewacin Najeriya Cikin Makonni Biyu, Hedikwatar Tsaro
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumin nasara a arewacin Najeriya cikin makonni biyu da suka gabata
- Hukumar sojin Najeriya ta baza dakaru a atisaye daban-daban a yankunan arewa guda uku
- Yayinda ake fama da ta'addancin Boko Haram a gabas, ana fama da yan bindiga masu garkuwa da mutane a yamma
Abuja - Hedikwatar hukumar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa dakarun soji sun halaka, ƴan ta'adda 77 a wasu hare-hare da suka kai daban-daban a yankunan Arewa maso Gabas, Arewa ta tsakiya da Arewa ta Yamma, a makonni biyu da suka gabata.
Manjo Janar Musa Danmadami, darektan watsa labarai na hukumar, shine ya bayyana haka a ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, a wajen taron watsa labarai kan ayyukan hukumar, wanda yake zuwa duk bayan mako biyu.
Danmadami yace dakarun sojin atisayen 'Operation Hadin Kai' a yankin Arewa maso Gabas, sun halaka ƴan ta'addan Boko Haram da ISWAP 56, sannan suka cafke ƴan ta'adda 26 da ceto mutum 59 da suka sace, a cikin mako biyu, rahoton DailyTrust.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bayyana cewa ɓangaren sojin sama ya halaka ƴan ta'adda da dama a wasu hare-haren sama da suka kai kwanan nan a maɓoyar ƴan ta'adda dake a Damboa, Tumbun Dila, Arege da ƙauyukan dake kusa da Yammacin Tumbuns a jihar Borno.
Danmadami yace ƴan ta'adda waɗanda yawan su yakai 340 da iyalan su waɗanda suka haɗa da matasa 12, mata 133 da yara 195 sun miƙa wuya ga dakarun a wurare daban-daban.
Ya kuma bayyana cewa dakarun sun farmaki wata maɓoyar ƴan ta'adda a ranar 27 ga watan Janairu, a ƙauyen Yuwe cikin ƙaramar hukumar Konduga ta jihar Borno, inda suka halaka ƴan ta'adda 17.
Dakarun kuma sun kwato bindiga mai sarrafa kanta guda ɗaya, gurneti 36 da harsasai guda 77 masu kaurin 7.62mm ƙirar NATO, riwayar Premium Times.
Arewa maso Gabas
A yankin Arewa maso Gabas, Danmadami yace dakarun sojin atisayen 'Operation Hadarin Daji' a cikin makonni biyu, sun halaka ƴan ta'adda 16 sannan suka cafke guda biyu a wurare daban-daban na yankin.
Yace dakarun sun kwato bindigogi 12 ƙirar AK47, bindigogin hannu 16 ƙirar gida, bindiga ɗaya ƙirar FN, da harsasai 48 masu kaurin 7.62mm.
Arewa ta tsakiya
A yankin Arewa ta tsakiya, Danmadami yace dakarun atisayen 'Operations Safe Haven Whirl Stroke' sun halaka ƴan ta'adda 5 da cafke guda 10 daga cikin su tare da wani mai siyar da bindigu.
Ya kuma bayyana cewa dakarun sun kwato shanaye 36, babura 10, wayoyin hannu guda uku, wuƙaƙe biyu da maɗaukan harsasai masu kaurin 7.62mm waɗanda babu komai a ciki.
Asali: Legit.ng