Atiku Ya Kaddamar da Makarantar Haddar Al-Qur’ani a Garinsu Ibrahim Shekarau

Atiku Ya Kaddamar da Makarantar Haddar Al-Qur’ani a Garinsu Ibrahim Shekarau

  • Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya halarci taron bude makarantar Al-Qur’ani a jihar Kano
  • Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Ibrahim Shekarau a gina katafariyar makarantar addinin Islama a jihar Kano
  • ‘Yan siyasa a Najeriya na ci gaba da kamfen don tallata kansu gabanin zaben 2023 da ke tafe nan kusa

Gezawa, jihar Kano - Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya halarci bikin bude wata makarantar haddar Al-Qur’ani a yayin yawon kamfen dinsa a jihar Kano.

Atiku ya jagoranci wannan kaddamar da makaranta ne a garin Gunduwawa da ke a karamar hukumar Gezawa ta jihar.

Rahoton da muka samo daga jaridar Aminiya na cewa, sanata mai wakilitar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ne ya gina katafariyar makarantar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu koli ta fadi sahihin dan takarar gwamnan APC a jihar Abia

An kaddamar da makarantar Al-Qur'ani a Kano
Atiku Ya Kaddamar da Makarantar Haddar Al-Qur’ani a Garinsu Ibrahim Shekarau | aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Hakazalika, an ce an lakkabawa makarantar sunan kakan sanatan; Gwani Muhammadu Dan Gunduwawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya girman makarantar yake?

An ruwaito cewa, makarnatar za ta dauki dalibai sama da 500, kuma an tsara daukar sabbin dalibai zubin farko maza 250 da mata 250 domin karantar dasu zallan ilimin Al-Qur’ani.

A bangaren tasirin karatu, ana kyautata zaton dalibai za su haddace littafin mai tsarki cikin watanni shida kacal.

Abin da Atiku ya tofa a yayin bude makarantar

Atiku Abubakar ya yabawa Shekarau bisa wannan babban aiki da zai kusantar da dalibai da ubangijinsu tare da habaka ilimin addinin Islama.

Sanata Shekarau kuwa ya godewa Atiku da wannan ziyara da kuma karfafa masa gwiwa, hakazalika da taimaka masa wajen bude makarantar.

Shekarau ya shaida cewa, babban burinsa shine samar da romon dimokradiyya ga al’ummar mazabarsa da kasa baki daya ta hanyoyi daban-daban.

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda Tinubu ya Ziyarci Mahaifiyar Marigayi ‘Yar’adua a Katsina

Idan baku manta ba, Atiku ya sauka a jihar Kano ne domin taron gangamin kamfen kasancewarsa dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ke tafe.

Tsaikon da za a samu a zaben 2023, cewar tsohon shugaban INEC

Yayin da 'yan siyasa ke ci gaba da kamfen, tsohon shugaban INEC ya bayyana kadan daga abin da ya hango game da zaben 2023 da ke tafe nan kusa.

Attahiru Jega ya ce, 'yan siyasa ne babban kalubalen da ke tattare da zaben bana, kasancewar har yanzu basu sauya halayensu ba.

Ya kuma ce, masu kada kuri'u ma kalubale ne, domin ba kowa ne ya hankalta da yadda zabe yake ba a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.