EFCC Ta Bukaci Kotun Daukaka Kara da Ta Dakatar da Batun Tasa Keyar Bawa Gidan Maza
- Hukumar EFCC ta nemi a yi watsi da batun kama shugabanta Abdulrasheed Bawa bayan umarnin kotu
- A gaban kotun daukaka kara, EFCC ta bayyana dalilanta na bukatar yin watsi da batun kotun Kogi
- A baya kun ji yadda kotu a jihar Kogi ta tasa keyar dangin gwamna Yahaya Bello, ana neman matarsa ruwa a jallo
FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta daukaka kan hukuncin da babbar kotun jihar Kogi ta yi na umarnin tasa keyar shugabanta, Abdulrasheed Bawa zuwa magarkama.
Mai shari’a R.O Ayoola na kotun Kogi a ranar Litinin ya umarci sufeto janar na ‘yan sandan Najeriya da ya kamo Bawa tare da tura shi magarkamar Kuje ya shafe kwanaki 14 a can.
Kotun ta zargi Bawa da kin bin umarnin kotu a lokuta mabambanta, lamarin da ya sa ta umarci a kawo shi gabanta, rahoton PM News.
Yadda batun ya soma tun farko
Alkalin ya nemi kama Bawa ne bisa saba wani umarnin kotu na ranar 30 ga watan Nuwamban bara, inda aka umarce shi da ya zo gaban kotu a wata kara ta Ali Bello.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bello ya maka Bawa a kotu ne bisa zargin ya sa an kama shi tare da tsare shi ba bisa ka’ida ba.
Ya kuma bayyana cewa, duk da umarnin kotu, hukumar ta EFCC karkashin Bawa ta ki sakinsa, inda aka ci gaba da rike shi da zargin yin sama da fadi da wasu kudade har na tsawon kwanaki uku.
Bukatar Bawa a gaban kotun daukaka kara
A bangare guda, EFCC ta shigar da kara a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar Talata, inda ta nemi a yi watsi da batun kama Bawa har zuwa lokacin da za a saurari karar a gaban kotun na daukaka kara, Premium Times ta ruwaito.
A hujjar EFCC, babbar kotun jihar Kogi bata da ikon sararan kara irin wannan, kasancewar kama Bello da tsare ya faru ne a Abuja ba a Lokoja ba.
EFCC ta kuma bayyana cewa, Bawa tuni ya fara neman cike takardun daukaka kara zuwa gaba, amma har kotun ta ba da umarnin kama shi takardun basu fito ba.
Ana neman matar gwamna da danginta bisa zargin almundahana
A wani labarin kuma, kun ji yadda wata kotu ta tasa keyar wani dangin gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a kotu bisa zargin almundahana.
Hakazalika, kotun ta bayyana neman matar Yahaya Bello bisa zargin tana da hannu a lamarin.
Ba wannan ne karon farko da ake zargin ahalin masu rike da mukamai a Najeriya da aikata almundahana ba.
Asali: Legit.ng