Kwastomomin Banki Sun Bukaci CBN Ya Saki Tsoho da Sabon Naira

Kwastomomin Banki Sun Bukaci CBN Ya Saki Tsoho da Sabon Naira

  • Kwasotomomin bankuna a Najeriya sun roki CBN ya ci gaba da sakin tsofaffi da sabbin takardun naira
  • Ta bakin kungiyarsu ta ƙasa BCAN, kwastomomin sun nemi haka ne bayan hukuncin Kotun koli jiya Laraba
  • Har yanzun 'yan Najeriya na fama da karancin takardun naira lamarin da ya gurgunta kasuwanci da rayuwar yau da kullum

'Yan Najeriya masu amfani da bankunan kasuwanci sun bukaci babban bankin ƙasa CBN ya sako masu tsofaffi da sabbin takardun naira domin su ci gaba da hada-hadar yau da kullum da su.

Ƙungiyar kwastomomin bankuna ta ƙasa (BCAN) ita ce ta bukaci haka daga CBN biyo bayan hukuncin da Kotun koli ta yanke ranar Laraba, 8 ga watan Fabrairu, 2023.

Sabbi da tsoffin kudi.
Kwastomomin Banki Sun Bukaci CBN Ya Saki Tsoho da Sabon Naira Hoto: CBN
Asali: UGC

Rahoton jaridar The Nation ya tattaro cewa kungiyar BCAN ta bakin shugabanta na ƙasa, Uju Ogubunka, ya ce matakin da Kotu ta ɗauka ya yi daidai duba da halin da mutane ke ciki.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Bankuna Sun Haɗe Kai, Sun Fitar da Sabuwar Sanarwa Ana Tsaka da Rashin Sabbin Kuɗi

Ya kuma bayyana cewa idan sabbi da tsofafin takardun N200, N500 da N1000 suka ci gaba da yawo wahalhalu zasu ragu kuma tattalin arzikin mutane zai bunƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, shugaban ƙungiyar kwastomomin banki, Mista Ogubunka, ya ce:

"A yanzu ya kamata CBN ya umarci bankunan kasuwanci su rika baiwa mutane tsofaffi da sababbin takardun naira lokaci zuwa lokaci domin kara yawan kuɗi a hannun al'umma."

Wane hukunci Kotun koli ta yanke?

A jiya Laraba, Kotun Koli ta umarci babban banki da ya dakatar da shirinsa na haramta amfani da tsoffin kuɗi daga ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023.

Kotun ta dauki wannan mataki ne bayan gwamnatocin jihohi uku sun kai karar gwamnatin tarayya kan sabon tsarin CBN na sauya wasu takardun naira, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Bugu da ƙari, awanni bayan wannan hukunci, Asusun ba da lamuni na duniya ya shawarci CBN ya duba yuwuwar ƙara wa'adin amfani da tsohon kuɗin saboda wahalar da yan Najeriya ke sha.

Kara karanta wannan

Tsawaita kashe tsoffin kudi: Abu 3 da kowa ya kamata ya sani game da hukuncin kotun koli

A wani labarin kuma Ma'aikata Sun Yi Barazanar Rufe Bankuna Kan Hare-Haren da Ake Kai Masu

Ƙungiyar ma'aikatan bankuna, Inshora da sauran ma'aikatun kuɗi a Najeriya sun ce ba zasu ci gaba da lamurtar harin da fusatattun yan Najeriya ke kai masu ba.

Zanga-zanga ta barke a wasu sassan Najeriya sakamakon wahalar karancin takardun kuɗi, lamarin da ya kai ga kai hari bankunan kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262