Rashin Wadatar Naira: Ku Shiga Ajin Koyon Dambe – Shehu Sani Ya Shawarci Ma’aikatan Banki

Rashin Wadatar Naira: Ku Shiga Ajin Koyon Dambe – Shehu Sani Ya Shawarci Ma’aikatan Banki

  • Jama’a na ci gaba da kokawa yayin da karancin sabbin takardun naira da wahalar man fetur ya ki ci ya ki cinyewa
  • Har ta kai yanzu yan Najeriya basa samun damar cire kudadensu daga na’urorin ATM sannan masu POS na chaji ba kadan ba yayin da mutum zai cire kudi
  • Da yake ba da shawara kan yadda ma’aikatan banki za su taimaki kansu a wannan mawuyacin lokaci, Shehu Sani ya bukace su da su shiga ajin koyon dambe na dare

Sanata Shehu Sani, dan siyasa kuma mai rajin kare hakkin dan adam, ya ba da shawara kan yadda ma’aikatan bankunan Najeriya za su taimaki kansu a wannan lokaci mai matukar wahala.

Yayin da yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan karancin sabbin takardun naira, sannan wasu fusatattun matasa ke ci gaba da yin zanga-zanga da farmakar bankuna, tsohon dan majalisar na Kaduna ya bukaci ma’aikatan banki da su shiga ajin koyon dambe (Judo ko Taekwando).

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

Takardun kudi da Shehu Sani
Rashin Wadatar Naira: Ku Shiga Ajin Koyon Dambe – Shehu Sani Ya Shawarci Ma’aikatan Banki Hoto: Senator Shehu Sani
Asali: Facebook

Yadda ma’aikatan banki za su iya kare kansu, Shehu Sani ya bayyana

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 9 ga watan Fabrairu, Sani ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A lokaci irin wannan, idan kai ma’aikacin banki ne, ka yi kokarin shiga ajin koyon damben Judo ko Takwendo na yamma, zai iya taimaka maka."

Jama’a sun yi martani

@streakme03 ta wallafa:

“Ina son yanayin abubunka yallabai, idan lamura suka zarce yin kuka kawai sai ka yi dariya don jin sauki a zuciya. Allah ya tausayawa Najeriya.”

@Sociallizee ya rubuta:

“Ma’aikatan banki ba sune matsalar ba, amma ta yaya zan yi bayanin haka ga yan uwana. Manyan manajojin sune suke boye sabbin naira.”

@Benzkovic001 ta wallafa:

“Kuma Judo zai taimakeka a kan adda ko kwalba.”

@EgwuSamuel49 ta wallafa:

“Kuma ki san yadda ake tsallake Katanga koda ke mace ce.”

Kara karanta wannan

Kaico: Daidai lokacin da zai kai 'ya'yansa makaranta, 'yan bindiga sun sheke lakcara a Anambra

@AdebolaAdeboye4 ya wallafa:

“Shawara mai kyau. Gara su bi shi.”

Karancin Naira: Masu POS na cin karensu ba babbaka, suna samun kudi a gidajen mai

A wani labarin kuma, mun ji cewa yayin da yan Najeriya ke fama da wahalar karancin kudi, masu POS suna gasawa jama'a hannu da chaji yayin cire kudi.

Kamar yadda suka bayyana, suna samun kudi ne daga gidajen mai bayan sun ba da na goro don haka suma suke chaji sosai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng