'Yan Siyasa da Masu Kada Kuri’u Ne Barazanar Zaben Bana, Cewar Tsohon Shugaban INEC Jega
- Farfesa Attajiru Jega ya tabo abin da ka iya zama barazana ga zaben 2023 da ke tafe nan da kwanaki kadan masu zuwa
- Jega ya ce ‘yan siyasa basu sauya hali ba, don haka za a ci gaba da yin duk mai yiwuwa don ganin an samu matsala a zabe
- A cewarsa, magudi ne babban makamin da ‘yan siaysa ke amfani dashi wajen lashe zaben, hakan babbar barazana ce ga zaben bana
FCT, Abuja - Gwani kan harkar zabe kuma tsohon shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Attahiru Jega ya bayyana abubuwan da ka iya zama tasgaro da barazana ga nasarar zaben 2023.
Ya yi magana ne yayin da yake tsokaci game da yadda zaben 25 ga watan Faburairu da na 11 ga watan Maris za su kasance, BBC ta ruwaito.
Ya yi wannan jawabin ne yayin taron wayar da kan jama’a game da zaman tare da zabe cikin lumana da cibiyar Da'awa da Tabbatar da Jin Dadin Jama'a ta babban masallacin tarayya da ke Abuja ta shirya.
Mutanen da sune barazana ga zaben bana
Jega ya bayyana cewa, ‘yan siyasa, musamman wadanda ke takara su ne na farko da ka iya zama barazana ga zaben bana, domin kuwa ba a samu wani sauyi ba ga yadda suke tafiyar da harkokin zabe tun 1999 ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa, burin ‘yan siyasa kawai su yi nasara ne ko ta halin kaka, don haka za su iya yin komai don ganin sun lashe zabe a matakai daban-daban.
A fahimtar Jega, ‘yan siyasa sun dauki yin nasara a zabe a matsayin wani lamari na ko a mutu ko a rayu, don haka har yanzu basu wani sauya halinsu ba.
Rashin hukunta 'yan siyasa yasa basu sauya hali ba
Ya bayyana kukan cewa, ba a hukunta ‘yan siyasa daga halayensu na banza da magudin zabe a iyakar saninsa.
Ya kuma kara da cewa, suna yin duk mai yiwuwa wajen ganin an yi magudi a zabe, wanda hakan barazana ce ga zaben bana.
Hakazalika, ya ce masu kada kuri'u ne rukuni na biyu da ka iya kawo tsaiko ga zaben na bana, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Za mu taimaka INEC ta yi zabe cikin tsanaki
A wani labarin kuma, gwamnan CBN ya ce zai ba da hadin kai wajen tabbatar da an yi zaben 2023 cikin kumana.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya gana da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu kan batun sabbin Naira da zaben 2023.
‘Yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da zaben bana, sabbin Naira sun yi karancin da ba a samunsu a kasar.
Asali: Legit.ng