Gwamna Umahi Ya Ayyana Goyon Baya Ga Buhari Game da Canja Naira
- Gwamna jihar Ebonyi, mamban APC ya nuna tsantsar goyon bayansa ga shirin canja takardun naira
- David Umahi ya bayyana cewa Buhari mutumin kirki ne wanda ba ya kaunar ganin ana wahalar da yan Najeriya
- Ana ta kai kawo kan tsarin sabon naira, shugaba Buhari ya zauna da masu ruwa da tsaki yau a fadarsa kan batun
Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kan batun canja takardun naira.
Umahi, wanda ya nuna yana da masaniyar halin da mutane ke ciki, yace cikin kankanin lokaci shugaban kasa zai share hawayen mutane domin yana da niyya mai kyau ga Najeriya.
Jaridar Tribune ta tattaro cewa Umahi ya faɗi haka ne a a wurin ralin kaddamar da kamfen APC wanda ya gudana a Ugbogo, ƙaramar hukumar Ebonyi ranar Talata.
A kalamansa, gwamna Umahi ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Buhari ya yi abubuwa masu tarin yawa a ƙasar nan, mutum ne mai zuciya mai tsafta, ina son faɗawa mutanen mu, muna tare da shugaban kasa kan batun canja kuɗi, nan gaba mu zamu ji dadin matakin da ya ɗauka."
"Mun san cewa ana fama da karancin (sabbin takardun naira) a jihar Ebonyi, mun san kp mun je banki babu kuɗin, kuma mun san ATM ya cika maƙil da jama'a, duk mun gaya wa shugaban kasa haka."
"Tuni shugaban ƙasa ya fara magance matsalar da ake fuskanta, ya kasance mutum mai kaunar talakawa, ya tsani jefa mutane cikin ƙangin wahala, ya kamata a bar mutumin kirki ya gama aikinsa."
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa wannan na zuwa ne a lokacin da wahalhalu suka ƙara tsananta kan karancin sabbin takardun N200, N500 da N1000 da CBN ta canja masu tsari.
Tun bayan bullo da wannan tsarin, babban banki da bankunan kasuwanci ke musayar yawu kan wanda ke da laifin jefa mutane cikin wahala, kamar yadda Independent ta rahoto.
Shugaba Buhari ya fara daukar matakan sawwaka wa mutane
A wani labarin kuma Buhari Ya Gana da Gwamnan CBN, Shugaban NGF, Bagudu Kan Karancin Naira
Sauran manyan jiga-jigan da suka halarci zaman sun haɗa da, gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele, shugaban hukumar yaƙi da cin hanci (EFCC), Abdulrasheed Bawa.
Wannan na zuwa ne kasa da mako ɗaya bayan gwamnonin APC sun sa labule da Buhari kan batun a fadar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng