Babu Wani Dan Najeriya Mai Tunani Da Zai Zabi APC Ko PDP, In Ji Kwankwaso
- Dan takarar shugabancin kasa a inuwar jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa duk wanda ya san me yake masa ciwo ba zai zabi PDP da APC ba
- Kwankwaso ya kuma roki magoya baya da su guji tada tarzoma lokacin zabe amma su zama masu sa ido
- Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya kuma roki yan Najeriya da su guji siyar da kuri'a a babban zabe mai zuwa na 25 ga Fabrairu
Dan takarar shugabancin kasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabi'u Kwankwaso, ya ce babu wani dan Najeriya da ya san ciwon kan shi da zai zabi daya daga cikin APC ko PDP a zaben shugaban kasa na 25 ga Fabrairu.
Kwankwaso ya bayyana haka ne ranar Litinin lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayan sa a wajen taron yakin neman zaben dan takarar gwamna da ya gudana a karamar hukumar Tarauni da ke Jihar Kano.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsohon gwamnan Jihar Kano Kwankwaso ya bayyana jam'iyyun biyu a matsayin makiyan mata da matasa da sauran yan Najeriya, jaridar The Punch ta rahoto.
Da ya ke jan kunnen magoya bayansa kan su guji tada tarzoma, ya ce jam'iyyar ba zata lamunci kowanne irin magudi ba a zabe mai zuwa.
Ya ce:
''PDP da APC sun mutu kuma duk wanda ya san me yake masa ciwo ba zai goyi bayan su ko ya sake zabar su ba.
''Su ne silar jefa Najeriya halin da ta ke ciki yanzu kuma makiya ne ga mata, matasa da sauran yan Najeriya. Saboda haka dole mu kada su.
''Ku zama masu son zaman lafiya kada a same ku da tada tarzoma, amma baza a maimaita mana abin da ya faru a zaben da ya gabata ba, don haka duk wanda ya kada mana kuri'a zai zama jami'in sanya ido, kayi zabe ka kuma tabbatar an kirga kuri'ar ka."
Ya kuma roki mazauna jihar da kuma yan Najeriya gaba daya da kada su kuskura su siyar da kuri'a.
Jagoran yakin neman zaben Kwankwaso da mutanensa sun fita daga jam'iyyar NNPP a Bauchi
A wani rahoto kun ji cewa wasu magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar jam'iyyar NNPP sun sauya sheka zuwa PDP.
Daily Trust ta rahoto cewa shugaban yakin neman zaben jam'iyyar ta NNPP da magoya bayansa sun zabi su goyi bayan Atiku Abubakar ne a 2023.
Asali: Legit.ng