Za'a Shiga Sabon Wahalar Mai, Kungiyar IPMAN Ta Umurci Mambobinta Su Rufe Dukkan Gidajen Mai A Najeriya

Za'a Shiga Sabon Wahalar Mai, Kungiyar IPMAN Ta Umurci Mambobinta Su Rufe Dukkan Gidajen Mai A Najeriya

  • Lamarin tsada da karancin na shirin daukan sabon salo a jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya
  • Sama da watanni biyar yanzu yan Najeriya na fama da tsada man fetur da kuma rashinsa gaba daya
  • Kamfanin man feturin najeriya NNPC Limited ya bayyana cewa akwai isasshen man fetur a ajiye

Borno - Kungiyar yan kasuwar mai masu zaman kansu, IPMAN shiyyar jihar Borno, ta umurci dukkan mambobinta su gaggauta rufe gidajen mansu a fadin jihar.

Shugaban kungiyar IPMAN na jihar, Mohammed Kuluwu, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya fitar ranar Talata.

Hakazalika Mohammed Kuluwu ya umurci mambobinsa su daina siyan mai daga wajen depot sai lokacin da hali yayi.

A cewar kungiyar:

"Halin da muke ciki na shafan saya da sayar da mai, sannan kuma wajabtawa mambobinmu sayar da mai a farashin da fadi zamu yi."

Kara karanta wannan

"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

Petur
Za'a Shiga Sabon Wahalar Mai, Kungiyar IPMAN Ta Umurci Mambobinta Su Rufe Dukkan Gidajen Mai A Najeriya
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bankuna, Gidajen Mai Da Yan Kasuwa Sun Dena Karbar Tsaffin Kudi A Jihar Arewa

A wan labarin kuwa, rahotanni daga Jihar Sokoto sun bayyana cewa bankuna da sauran wuraren kasuwanci sun daina karbar tsohon kudi

Wani ma'aikacin banki ya shaida cewa matakin na zuwa ne biyo bayan umarnin da babban bankin kasa CBN ya turo da shi

Al'umma na cigaba da kokawa kan yadda gwamnatin tarayya ta ki jin koken talakawa akan batun chanjin kudi

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida