Akwai Matsala: Basarake Ya Ga Abun Mamaki Yayin da Ya Je Bankin Neman Sabbin Kuɗi

Akwai Matsala: Basarake Ya Ga Abun Mamaki Yayin da Ya Je Bankin Neman Sabbin Kuɗi

  • 'Yan Najeriya na ci gaba da wahala wajen neman sabbin kuɗin da CBN ya canja domin tafiyar da harkokinsu na yau da kullum
  • A jihar Ogun, reshen bankin GT a Abeokuta ya kunyata wani Basaraken gargajiya yayin da ya je neman sabbin takardun ranar Litinin
  • Gwamnan babban bankin Najeriya ya ce babu wanda zai yi asarar kuɗinsa sakamakon wannan sabon tsarin

Ogun - Sarkin gargajiya na Ijaiye-Titun a jihar Ogun, Nofiu Adeyemi, na ɗaya daga cikin dandazon kwastomomin da aka kora daga cikin reshen bankin Guaranty Trust (GT), Abeokuta.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Basaraken ya je bankin ne tare da mutane masu dumbin yawa a kokarin neman samun sabbin takardun kuɗi ranar Litinin.

Takardun sabbin naira.
Akwai Matsala: Basarake Ya Ga Abun Mamaki Yayin da Ya Je Bankin Neman Sabbin Kuɗi Hoto: CBN
Asali: UGC

Meya faru har aka haɗa da Basaraken?

Mista Adeyemi ya isa harabar bankin, wanda ke hannun riga da Sakatariyar yan jarida (NUJ) a Oke-Ilewo, Abeokuta, babban birnin Ogun, inda ya tarad da dandazon jama'a suna dakon cire kuɗi.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Mamayi Banki Ba Zato Ba Tsammani, Ya Dauki Mataki Mai Daɗi Ga Mutane Kan Sabbin Kuɗi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga zuwansu, Jama'a suka buɗa masa hanya ya wuce kai tsaye kasancewarsa Uba kuma Basaraken da suke martabawa amma duk da haka ma'aikatan bankin suka ƙi saurarensa.

Duk da karamcin da kwastomomi suka nuna wa Basaraken na buɗa masa hanya ya isa kofar shiga Bankin, ma'aikatan dake kallon duk abinda ke faruwa ta CCTV ba su saurare shi ba balle su bude masa ƙofa.

Bayan kwankwasa kofar da jiran tsawon mintuna 30 ba'a bude ba, Basaraken da aka ba kunya, ya koma motarsa ya bar harabar bankin.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tun da sanyin safiya misalin karfe 6:30 mutane duka taru amma babu wanda ya samu ikon shiga cikin harabar bankin.

Mutane sun kutsa da tsiya cikin GT

Bayan jiran dogon lokaci shiru babu wani bayai mai daɗi, dandazon mutane suka kutsa da tsiya cikin Bankin lamarin da ya tilastawa ma'aikata fitowa suka masu bayanin babu tsabar takardun kuɗi.

Kara karanta wannan

Bayani Dalla-Dalla: Wace Rana Tsohon Kudi Zai Daina Aiki, 10 Ko 17 Ga Wata? Wane Bankuna Zasu Karba Idan Wa'adi Ya Cika?

Kwastomomin, wanda suka ƙunshi mata masu shayarwa, nan take suka fara wata kwarya kwaryan zanga-zanga kuma suka sha alwashin ba inda zasu sai an bari sun cire kuɗi.

Wasu daga cikin kwanstomomin sun bayyana cewa karancin takardun sabbin kuɗin sun jefa da yawan mutane cikin halin lahaula.

Jaridar Punch tace ganin halin da mutane suka tsinci kansu, gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya zauna da masu ruwa da tsaki a CBN don magance matsalar.

Abinda ya kamata ku sani

A wani labarin kuma Shin yaushe ne ainihin wa'adin CBN tsakanin 10 da 17 ga wata? Wane bankuna zasu karbi tsohon kuɗin mutane bayan haka, mun tara maku amsoshin abubuwan da suka shiga masu duhu.

Idan baku manta ba, gwamnan CBN ya shaida wa majalisar wakilan tarayya cewa bankuna zasu ci gaba da karban tsohon kuɗi ko bayan wa'adi ya cika.

A cewarsa, babu wani ɗan Najeriya da zai yu asarar tsohon kuɗin da ya sha wahala wajen samu, sun bullo da tsaruka masu kyau.

Kara karanta wannan

Assha: Na Kusa Da Buhari Sun Fi Damuwa Da Batun Sauyin Kudi, Minista Ya Bayyana Gaskiyar Abin da Ke Ransa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262