Jami’an NDLEA Sun Kama Mata Mai Juna Biyu Da Miyagun Kwayoyi A Cikin Rediyo

Jami’an NDLEA Sun Kama Mata Mai Juna Biyu Da Miyagun Kwayoyi A Cikin Rediyo

  • Wata mata mai dauke da juna biyu ta fada komar NDLEA bayan da tayi kokarin safarar miyagun kwayoyi
  • Matar wanda ta kunshe wiwi a cikin kananan rediyo guda biyu, tayi nufin aika kayan Dubai kafin ta shiga hannu
  • Jami'an NDLEA na ci gaba da yunkuri wajen dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi kamar yadda kakin su na Lagos ya bayyana

Legas - Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da ke sansanin fita da kaya ta NAHCO shiyyar filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad, da ke Ikeja, Lagos, sun kama wata mata mai juna biyu, Mrs Sylvester Gloria Onome, ranar Litin, 30 ga watan Janairu, 2023, saboda samun ta da miyagun kwayoyi.

Mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ranar Lahadi a Abuja ya ce an kama matar da giram 800 na wiwi da aka boye a cikin kananan rediyo da za a tura Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

Wacce ake zargi
Jami’an NDLEA Sun Kama Mata Mai Ciki Da Miyagun Kwayoyi a Cikin Rediyo. Hoto: Vanguard NGR
Asali: Facebook

Duk a ranar, Hukumar NDLEA ta kuma dakatar da wasu kayan da aka tura jamhuriyyar Congo, Kinshasa, dauke da kwalabe 111 da mayukan shafawa da aka boye kilo 24.50 na ephedrine, wani sinadari da ake amfani da shi wajen hada methamphetamine.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babafemi ya ce:

''An bibiyi sahun kayan inda aka kama wani dan tireda a kasuwar bajakolin Alaba, dake yankin Ojo a Lagos, Onyekachukwu Uduekwelu, bayan damke wasu jami'an tura kaya biyu tun da fari''

An kama wata matar aure dauke da miyagun kwayoyi

A ranar Juma'a, 27 ga Janairu, an kama wata matar auren, Mrs Okpara Chizoba Victoria, a gidan ta mai lamba 37, Obashola street, a yankin Ijesha na Jihar Lagos, bayan kwace giram 300 na wiwi da aka boye a jakar busasshen kifi da za a aika Dubai, hadaddiyar daular larabawa ta hannun jami'in aika sako.

Kara karanta wannan

Lauyoyi sun fusata da yadda 'yan bindiga suka kashe alkali yana tsaka da yanke hukunci

Haka hukumar ta dakile safarar wasu miyagun kwayoyi masu yawa, musamman hodar iblis, heroin, methamphetamine da ephedrine da za a tura Dubai, UAE da kuma nahiyar turai ta hanyoyin basaja da yawa daga wajen manyan dilolin miyagun kwayoyi ta MMIA dake Ikeja a Lagos, jami'an NDLEA sun yi nasarar dakile wa tare da kama masu laifin.

A cewar rahoton The Cable, daga cikin manyan da suka hannu akwai wani dan Najeriya mazaunin Athens, a kasar Greece, Iwuodur Edward Chinedu.

Ya fada komar hukuma ne a jirgin Ethiopian airline ranar Juma'a, 3 ga Fabrairu, bayan da jami'an NDLEA na filin jirgi suka wasu jakunkuna biyu lokacin gudanar da binciken da ake kafin hawa jirgi.

Lokacin da ake bincika jakar a gaban Chinedu da sauran jami'an filin jirgi, an samu wasu manyan curi guda biyu an nade su da takardar foil da kuma barkono da aka warwatsa a saman jakar da kowanne bangaren jakar.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Fusatattun Matasa Yan Zanga-Zanga Sun Kai Hari Ofishin Gwamna

An yi amfani da curin don tsayar da jakar kuma an samu wasu kayyayaki da ke dauke da hodar iblis da kuma heroin da nauyin su ya kai kilo 1.30 da kuma giram 900, kowanne.

A cewar Babafemi:

''Yayin da yake amsa tambayoyi, Chinedu ya ce ya zo Najeriya ne wata uku da suka gabata domin ayi masa tiyata, wadda shi bai yadda anyi masa a Athens ba. Ya kuma ce an bashi jakar ne don ya kai kasar Greece akan kudi Naira miliyan 2."

An kama dagajin kauye kan zargin sayar da wiwi da miyagun kwayoyi

A wani rahoton, hukumar ta NDLEA ta kama dagacin kauyen Ruga, a karamar hukumar Shagari kan zargin safarar sayar da miyagun kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164