Karancin Naira: Masu POS Na Siyan Sabbin Naira Daga Gidajen Mai a Jihar Neja

Karancin Naira: Masu POS Na Siyan Sabbin Naira Daga Gidajen Mai a Jihar Neja

  • Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsi da kunci saboda rashin takardun kudi a gari
  • Masu POS da dama sun rufe harkokinsu inda wasu suka koma ga gidajen mai don samun kudi a hannunsu bayan sun basu na goro
  • A yanzu gidajen mai na cin kasuwarsu a garin Minna da ke jihar Neja inda suke siyar da kudi ga masu harkokin da ya danganci hada-hadar kudi

Niger - Wasu masu yin POS a garin Minna, jihar Neja sun bayyana yadda suke gwagwarmaya don ganin harkokin kasuwancinsu bai durkushe ba a yanzu da ake fama da karancin takardun kudi a gari.

A yanzu masu yin wannan harka ta POS suna siya sabbin naira ne daga gidajen mai don ci gaba da sanarsu.

Sabbin kudi
Karancin Naira: Masu POS Na Siyan Sabbin Naira Daga Gidajen Mai a Jihar Neja Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Wani mai aikin POS mai suna Mohammed Isah, ya fada ma jaridar Daily Trust cewa koda dai sai mutum yana da hanya ko alaka da masu gidajen man, ya yi nasarar samun N150,000 sau biyu a ranakun Asabar da Lahadi don cika muradin kwastamominsa.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun koma kwana gindin ATM saboda tsananin rashin kudi

Ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An yi mun chajin wasu kudade a wani gidan mai kafin na samu wadannan yan kudaden da nake baiwa kwastamomina. Ba abu ne mai sauki ba, amma ba mu da zabi. Saboda haka, don ganin kowa ya samu kudin, ina ba kwastama N5,000 sannan na chaje shi N150 kan kowani N1,000."

Ya bayyana cewa samun sabbi da tsoffin kudaden daga banki yana da matukar wahala; da chaji da yawa, lamarin da yasa masu harkokin POS da dama rufe kasuwancinsu.

Martanin wata ma'aikaciyar gidan mai

Legit.ng ta tuntubi wata ma'aikaciyar gidan mai wacce ta nemi a sakaya sunanta a nan garin Minna inda ta tabbatar da hakan.

Ta ce:

"Tabbass haka ne wasu mutane kan zo su karbi cinikin da muka yi don samun damar gudanar da harkokinsu. Su kan bamu N5000 kan kowani N100,000 da muka basu imma tsoffin kudi ko sabbi.

Kara karanta wannan

Masu POS sun Fallasa Wadanda ke SIyar Musu Kudi da Tsadar Har Suke Zugawa Jama'a Riba Mai Yawa

"Wannan ni a ganina aikin taimakon kai ne ba wani abu ba domin su kansu banki suna tsatsar mutane kafin su basu kudaden, idan ka ma kwatanta da namu a garabasa muke basu."

ICPC ta kai samame banki, ta bankado sabbin kudi boye a durowa

A wani labarin, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta bankado sabbin kudi boye a cikin durowan wani banki.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da karancin sabbin kudi a kasar lamarin da ya sa ICPC shiga aiki don tabbatar da wadatar kudi a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng