Sabon Sarkin Dutse: Muhimman Abubuwa da Ya Dace a Sani Game da Matashin da ya Gaji Mahaifinsa
- Gwamnatin jihar Jigawa ta nada mai martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi a matsayin sarkin Dutse na 22, bayan mahaifinsa ya kwanta dama a asibitin Abuja ranar Talata
- An haifi sabon sarkin a shekarar 1979, kuma ya yi digirinsa da digirin digir a jami'ar Monash (MUFY) Sunway College Campus da ke Malaysia
- Nadin ya biyo bayan amincewar majalisar nadin sarki na Dutsen inda aka lallasa Galadiman Dutse, Basiru Muhammad da yayan marigayin sarki a zaben
Dutse, Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da nada Hameem Nuhu a matsayin Sarkin Dutse na 22 a Jihar.
Ya gaji mahaifinsa Nuhu Muhammad Sanusi wanda ya kwanta dama ranar Talata a asibitin Abuja bayan kwashe shekaru 28 a karagar mulki.
Nadin ya biyo bayan kada kuri'un sirri da masu zabar sarkin Dutse suka yi.
Sauran 'yan takarar da suka kunshi Galadiman Dutse, Basiru Muhammad Sanusi, da yayan marigayin sarki, basu kai labari ba yayin zaben sarkin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka zalika, hukumar nada Sarakunan Jihar Jigawa ta amince da zabar Nuhu Sanusi wanda gwamna ya amince da hakan ranar 5 ga watan Fabrairu, jaridar Premium Times ta rahoto.
Har zuwa nada shi Sarkin Dutse, Nuhu Sanusi karami ya rike sarautar Dan'iyan Dutse.
Sabon sarkin shi ne Manajan Darakta HMS Energy Limited. Ya yi aiki da SMD consulting daga 2011 zuwa 2016 a matsayin Shugaban yankin arewa.
Ya rike mukamin shugaban bunkasa kasuwanci a Bilyak Consulting daga 2007 zuwa 2011.
An haifi sabon sarki a shekarar 1979, Sanusi ya yi digiri da digirin digir a Jami'ar Monash (MUFY) Sunway College Campus da ke Malaysia.
Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru ya taya Sanusi murna bisa nadinsa gami da masa fatan nasara da kwanciyar hankali a karagarsa matsayin Sarkin Dutse.
Allah yayi wa Mai Martaba Sarkin Dutse rasuwa
A wani labari na daban, mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi ya kwanta dama a ranar Talata da ta gabata.
Ya rasu yana da shekaru 79 bayan kwashe shekaru 28 kan karagar mulkin masarautar.
Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi ya rasu a wani asibiti a Abuja bayan fama da yayi da rashin lafiya na gajeren lokaci.
An yi jana'izarsa kamar yadda addini ya tanadar a ranar Laraba a garin Dutse inda manyan mutane suka samu halarta.
Asali: Legit.ng