Sabon Sarkin Dutse HRH Hammem Nuhu Sanusi Ya Shiga Fada

Sabon Sarkin Dutse HRH Hammem Nuhu Sanusi Ya Shiga Fada

  • Gwamnan jihar Jigawa ya aika wasika ta musamman ga sabon sarkin Dutsen da ya nada yau
  • Sabon sarkin masarautar Dutse mai tarihi ya shiga fada karon farko matsayin zababben sarki
  • Hammem Sanusi.ya rike matsayin Iyan Dutse lokacin rayuwar mahaifinsa Sarki da ya rasu

Dutse - Sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Abdulkadir Fanini, a ranar Lahadi ya gabatar da wasikar nada sabon sarkin Dutse ga Hammem Sanusi.

Zaku tuna cewa gwamnan jihar Jigawa, ya amince da nadin da babban 'dan marigayi sarkin Dutse ya maye gurbin mahaifinsa bayan zaben da kwamitin nadin sarki yayi a masarautar Dutse.

Gwamnan ya yi kira ga sabon sarkin ya gudanar da mulkinsa ta yadda al'ummarsa zasu ji dadi ba tare nuna bangaranci ko fifiko ba, rahoton DailyNigerian.

Sarki
Sabon Sarkin Dutse HRH Hammem Nuhu Sanusi Ya Shiga Fada Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Gwamnan Jigawa Ya Nada Sabon Sarkin Dutse

Gabanin nada shi sabon sarki, Hammem Sanusi.ya kasance yana rike da mukamin Iyan Dutse.

A cewar wani sashen wasikar:

"A madadin gwamnatin jihar Jigawa, mai girma gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya taya Alhaji Hameem Nuhu Sanusi murna bisa nadin da akayi masa kuma yana masa fatan alheri matsayin Sarkin Dutse."

Jawabin sabon Sarki

Sabon sarkin a jawabinsa, ya bayyana godiya ga gwamnan bisa amincewa da bashi wannan kujera.

Sarkin ya yi alkawarin damawa da kowa kuma yana neman goyon bayan kowa da kowa a masarautar.

Kalli hotunan:

Sarki
Sabon Sarkin Dutse HRH Hammem Nuhu Sanusi Ya Shiga Fada
Asali: Facebook

Sarki
Sabon Sarkin Dutse HRH Hammem Nuhu Sanusi Ya Shiga Fada
Asali: Facebook

Sarki
Sabon Sarkin Dutse HRH Hammem Nuhu Sanusi Ya Shiga Fada
Asali: Facebook

Sarki
Sabon Sarkin Dutse HRH Hammem Nuhu Sanusi Ya Shiga Fada
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel