Yanzu Yanzu: Gwamnan Jigawa Ya Bayyana Sabon Sarkin Dutse

Yanzu Yanzu: Gwamnan Jigawa Ya Bayyana Sabon Sarkin Dutse

  • Yan kwanaki bayan rasuwar tsohon Sarki Nuhu Muhammad Sunusi, Muhammad Hameem ya zama sabon Sarkin Dutse
  • Gwamna Badaru Abubakar ya amince da nadin Muhammad Hameem daga cikin mutane uku da suka nemi takarar kujerar
  • Kafin tabbatar da shi, masu zaben sarki sun aika sunansa majalisar sarakuna ta jihar inda suma suka yi mubaya'a

Jigawa - Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na na jihar Jigawa ya amince da nadin Muhammad Hameem a matsayin sabon sarkin Dutse.

Muhammad Hameem ya gaji Sarki Nuhu Muhammad Sunusi, wanda ya kwanta dama a makon jiya a wani asibitin Abuja, Daily Trust ta rahoto.

An nada sabon sarkin Dutse
Yanzu Yanzu: Gwamnan Jigawa Ya Bayyana Sabon Sarkin Dutse Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Mutum uku ne suka yi takarar kujerar

Jaridar ta tattaro cewa masu nada sarki a masarautar Dutse sun hada kai sun zabi sabon sarkin cikin masu takarar kujerar sarautar guda uku.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Budewa Tsohon Ministan Buhari Wuta, Mutum Biyu Sun Mutu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wata sanarwa daga majalisar masarautar ta ce an mika sunan sabon sarkin majalisar sarakunan jihar Jigawa wacce ita ma ta amince da hukuncin masu nada sarkin

Bayan nan majalisar sarakunan ta mika sunayen Muhammad Hameem da sauran yan takarar biyu ga gwamnan jihar don samun yardarsa, rahoton Aminiya.

Sanarwar ta ce:

"Daga baya gwamnan ya amince da nadin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon sarkin Dutse wanda ya fara aiki daga yau 05/02/2023.”

An yi jana'izar marigayi sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi

Idan za ku tuna, a ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu ne aka yi jana'izar mariyi sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, inda aka sada shi da gidansa na gaskiya.

Taron jana'izar marigayin ya samu halartan manyan sarakunan Arewa ,manyan yan siyasar Najeriya, manyan malaman addini da kuma yan'uwa da abokan arziki.

Kara karanta wannan

Ku Cigaba da Bin Layi Ba Zamu Kara Wa'adin Naira Ba Bayan Ranar 10 ga Febrairu, Gwamnan CBN

Basaraken kasar yarbawa ya zama dan fim

A wani labari na daban, mun ji cewa babban basaraken kasar Yarbawa, Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya bayyana a cikin wani shirin fim na masana'antar shirya fina-finai ta kasar Amurka wato Hollywood.

A cikin shirin fim din mai suna ‘Take Me Home’, Oba Adeyeye Ogunwusi ya fito ne a matsayinsa na sarki wato Ooni na Ife. Kuma shahararren fim din wanda ake kyautata zaton zai kayatar da jama'a ya fito da abubuwan tarihi na hakika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: