Matashi Ya Isa Gaban Rumfar ATM Da Katifa, Matashi, Tukunyar Gas Da Tukunya, Ya Yi Kalaci a Bidiyo
- Wani matashi ya ja hankalin jama'a da dama bayan wani abun mamaki da ya aikata a bakin rumfar ATM da ke Asaba
- Ba tare da ya ji kunyar kowa ba, matashin ya isa wajen da katifa, matashi, tukunyar gas da kunyar girkinsa sannan ya baje kamar yana gidansa
- Yayin da wani a wajen ya fitar da abincinsa, an gano matashin kishingide a kan katifarsa yana kalaci
Wani matashi dan Najeriya ya yi fice a soshiyal midiya bayan ya isa gaban rumfar ATM da katifa, matashi, tukunyar gas da kuma tukunyarsa na girki.
Lamarin wanda ya afku a gaban wani na'urar ATM da ke Asaba, babban birnin jihar Delta ya ba mutane da dama da ke layi a gaban na'urar mamaki.
A wani dan gajeren bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano matashin baje kamar yana cikin gidansa yayin da yake cin biredi da kosai.
An gano wani mutum da ke tare da shi yana fitar da taliya danya daga leda kamar dai mai shirin girki a kan tukunyar gas din.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Masu amfani da ATM din sun fitar da wayoyinsu yayin suka dungi daukar bidiyon mutumin da abokinsa. Bidiyon ya haifar da martani masu ban dariya.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
glorynwoke619 ta ce:
"Allah ya kyauta, nishadin da ke tattare da lamarin na kara kaiwa wani mataki, dan Allah su dage zaben don na fara jin dadin nishadin."
user5309050608166 ya ce:
"Mu dan kara hakuri dan Allah na dan lokaci ne amma Emefiele da shugaban kasa sun yi abun da ya dace a lokacin da bai dace ba."
Mercy t"Ana ce:
"Wani endsars din na zuwa a watan zabe. wannan ba alama bace mai kyau. Suna so su dage zaben ne."
comfortpius1 ta ce:
"Shiyasa nake son kasar nan, abun da ya kashe sauran kasashe ba zai iya kashe mu ba? saboda a kodayaushe muna neman hanyar kwantar da hankulanmu maimakon hawan jini."
ICPC ta kai samame wani banki, ta ga sabbin kudi da aka adana a durowa
A wani labarin kuma, mun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta kai samame wani banki a kokarinta na tabbatar da wadatar takardun naira a kasar inda ta tarar da sabbin kudi ajiye a cikin durowan bankin.
Asali: Legit.ng