Bidiyon Yaro 'Dan Najeriya Yana Shan Gari Cike da Annashuwa ya Janyo Cece-kuce
- Bidiyon wani yaro yana shan garin kwaki a makaranta lokacin karin kumallo ya girgiza zukatan jama'a da dama
- Mutane da dama sun labarta yadda suka fuskanci hakan yayin da suke kanana, wanda a cewarsu shan garin kwaki a cikin abokai abu ne mai dadi
- 'Yan Najeriyan da suka tausaya wa yaron sun nuna sha'awar tallafa mishi da danginshi don su fi haka rufin asiri
Wata malamar makaranta, @ifunanys, ta wallafa wani bidiyo da ke nuna daya daga cikin dalibanta ya jika garin kwaki yayin karin kumallo a makaranta.
Yaron ya ci abincinsa ba tare da damuwa da masu kallonsa ba. Malamar ta hasko fuskar yaron.
Mutane da dama sun labarta yadda suka fuskanci irin halin da yaron ya ke ciki.
Mutane da dama sun yi martani game da bidiyon, inda suka tambayi malamar ko ta bashi wani abinci mai kyau da yafi garin rogo, maimakon kawai yin bidiyon TikTok, inda ta amsa da "Eh".
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Akwai wata yarinya a kujerar gaba da ta tabbatar da ba'a dauki bidiyon abincinta ba yayin da ta kamkame shi da hannunta.
Daga lokacin da aka tattara wannan rahoton, bidiyon ya janyo martani sama da 300 da jinjina sama da 7,000.
Martanin 'yan soshiyal midiya
Ga wasu daga cikin martanin'yan soshiyal midiya:
Dolly Ava ta ce:
"Ya kike so danginshi su ji idan suka ga wannan."
Suc Cess001 ta ce:
"Amma shan garin kwaki ba wani abun mara kyau bane."
precious ta ce:
"Ina fatan bayan yin wannan bidiyon za ku siya masa abinci mai kyau."
Malamar ta yi martani:
"Na yi hakan. Nagode da tambaya."
Louis ta ce:
"Kai me yasa ki ka mishi bidiyo? Hakan ba abu bane mai kyau."
Bidiyo mai Narka Zuciya: Yara Marayu Suna ta Tsalle da Murna a Bidiyo, Suna Hayewa Jikin Mai Kula Dasu Bayan Ya Dawo Daga Tafiya
uaer1920301563097 ya ce:
"Zai zama jagora da kuma miji na gari wata rana."
Stephanie's ta ce:
"Yana cin abun da iyayensa suke da shi ne tare da godewa da abun da suka bashi."
SAMUEL ta ce:
"Wa ce ce mahaifiyar wannan yaron , mahaifiyarsa ta kawo min shi zan taimake shi!"
its kwen Diana ta ce:
"Ya na jin dadin shi kina mishi bidiyo. Haba ki bar yaron ya ci abinci hankali kwance mana."
Marayu sun tsalle tare da dafe mai kula da su bayan ya dawo daga tafiya
A wani labari na daban, wasu yara marayu sun yi abinda ya taba zukatan jama'a inda aka dinga martani.
Yaran sun dinga tsallen murna da ihu tare da cafe wanda ke kula da su bayan da ya dawo daga tafiya.
Asali: Legit.ng