'Yan Arewa Ba Za Su Zabe Ka Ba, Shugaban Yarbawa Ga Bola Tinubu

'Yan Arewa Ba Za Su Zabe Ka Ba, Shugaban Yarbawa Ga Bola Tinubu

  • Kungiyar Yarbawa a Kudu maso Gabas ta shaidawa Tinubu cewa, ya daina haba-haba da 'yan Arewa
  • Shugaban Afenifere ya ce, 'yan Arewa ba za su zabi Tinubu ba, ya dawo ya bi sahun Peter Obi a zaben 2023
  • Kungiyar ta Yarbawa dama ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour

Shugaban kungiyar Yarbawa ta Afenifere, Pa Ayo Adebanjo ya bayyana a ranar Asabar cewa, dan takarar shugaban na APC Bola Tinubu ya saka a ransa cewa, ‘yan Arewa ba zabansa za su yi ba.

Adebanjo ya bayyana bukatar Tinubu ya janye takararsa ta shugaban kasa tare da mara wa Peter Obi na jam’iyyar Labour baya a zaben bana, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya yi magana ne lokacin da yake tare da mamban Afenifere, sanata Femi Okunronmu yayin gangamin kamfen LP na shugaban kasa a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Zaben Shugaban Kasa Na 2023: "Da Izinin Allah, Wannan Ne Magaji Na", Buhari Ya Bude Baki Ya Magantu

'Yan Arewa ba za su zabe ka ba, inji Afenifere
'Yan Arewa Ba Za Su Zabe Ka Ba, Shugaban Yarbawa Ga Bola Tinubu | Hoto: pulse.ng
Asali: UGC

Kamfen da aka gudanar a Ake Palace ta samu halartar Peter Obi, abokin takararsa, Yusuf Datti Baba-Ahmad, shugaban LP na kasa, Julius Abure da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban Yarbawa ya caccaki Tinubu

Da yake magana ga jama’ar da suka halarci taron, Adebanjo ya yi magana da Yarbanci, inda ya caccaki Tinubu da kuma bayyana akwai yiwuwar faduwarsa.

Ya ce, Tinubu ya kamata ya janye takara, ya bi sahun Obi/Datti, inda yake ‘yan Arewa da yake ta bibiya yana zuba kudi za su bashi kunya a zaben na bana, Pulse ta tattaro.

Shugaban na Afenifere ya siffanta jam’iyyar Labour a matsayin jam’iyyar gamayya ta dimokradiyya, wacce za ta hada kan ‘yan kasar tare da kubutar dasu daga kuncin mummunan shugabanci.

A tun baya, kungiyar ta Yarbawa ta yi watsi da burin Tinubu, inda ya bayyana goyon baya ga dan takarar shugaban kasa daga Kudu maso Gabas, Peter Obi.

Kara karanta wannan

Magana ta Fara Fitowa: El-Rufai Ya Yi Karin Haske Kan Manyan da ke Yakar Takarar Tinubu

Tinubu ne zai gaje da yardar Allah, inji Buhari

A wnai labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya bayyana cewa, zai ci gaba da yiwa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu kamfen don zama magajinsa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a gaban dandazon jama’a a lokacin taron kamfen na APC a Lafia Square, jihar Nasarawa, inda ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu da Shettima a zaben 2023.

A baya can, Buhari ya ce zai yiwa Tinubu kamfen a jihohi akalla 10 a Najeriya don tabbatar da ya gaje shi a zaben da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.