Jerin Manyan Abubuwa 4 Da Ka Iya Kawowa Zaben 2023 Mushkila

Jerin Manyan Abubuwa 4 Da Ka Iya Kawowa Zaben 2023 Mushkila

Yayinda ake saura kasa da kwanaki 20 zaben shugaban kasan Najeriya, masu ruwa da tsaki sun bayyana damuwarsu game da abubuwan da ka iya zama kalubale ga zaben.

Za ayi zaben shugaban kasa da yan majalisar dokokin tarayya ranar 25 ga Februaru 2023 kuma ayi da gwamnoni da yan majalisar jihohi ranar 11 ga Maris, 2023.

Ana fargaban idan ba;a magance wadannan matsaloli ba, zaben zai fuskanci babban kalubale da ka iya zama tarnaki ga zaben.

Mun tattaro muku jerin abubuwa 4 da ka iya kawo tarnaki zaben bana

1. Rashin Tsaro

Kowani sashen kasar nan na fama da matsaloli na rashin tsaro daban-daban.

Wannan zai shafi rashin iya isan kayayyakin zaben INEC wasu lunguna da sako, hakazalika zai iya baiwa yan siyasa damar murde zabe a wadannan wurare.

Kara karanta wannan

Shin karancin Naira zai shafi zaben bana? Jami'in INEC ya yi gargadi mai daukar hankali

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayinda ake fama da harkar Boko Haram/ISWAP a Arewa maso gabas, ana fama da matsalar masu garkuwa da mutane a Arewa maso yamma.

A kudu maso yamma yan bindiga na addaban mutane, hakazalika a arewa maso tsakiya inda rikicin manoma da makiyaya yaki ci, yaki cinyewa.

A kudu maso gabas kuwa, rikicin yan awaren Biyafara IPOB na cigaba da sanadin asaran rayuka.

Hukumar INEC da kanta ta bayyana cewa:

"Idan ba'a magance matsalar rashin tsaro ba, wannan zai iya zama abinda zai sa a soke zaben ko a dage a wasu mazabu kuma hakan zai hana iya sanar da sakamako."

2. Tsadar man fetur

Sama da watanni biyar yanzu yan Najeriya na fama da tsada da karancin man fetur.

Layukan mai sun yawaita cikin birane yayinda farashin ya ninku har sau uku a karkara.

Kara karanta wannan

Ba Gwamnan Arewan da Zai Iya Kawowa Tinubu Kuri'un Jiharsa, Tsohon Shugaban NHIS

Kwanaki baya INEC ta garzaya har ofishin NNPCL domin kai kukanta.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyanawa shugaban NNPC wannan batu.

Mele Kyari yace su kwantar da hankalinsu wannan ba matsala bane, zai magance.

Ekiti
Jerin Manyan Abubuwa 4 Da Ka Iya Kawowa Zaben 2023 Mushkila
Asali: Original

3. Katunan zaben PVC

Dubunnan yan Najeriya har yanzu basu samu nasarar karbar katunan zaben watau PVC dinsu ba.

Mutane da dama sun kwashe sa'o'i a layin karban PVC amma duk da haka basu samu ba. Rahotanni sun bayyana cewa wasu jami'an INEC har cin hanci suke karba hannun mutane kan basu katunan su.

Sau biyu kenan INEC na dage ranar daina karbar katunan.

Har yanzu miliyoyin yan Najeriya basu karbi katunansu ba.

4. Sauya fasalin Naira

Sauya fasalin Naira ya jefa miliyoyin yan Najeriya cikin tsananin karanci da wahalar rayuwa.

Gwamnatin tarayya ta karbi tsaffin kudin hannun mutane kuma ta ki buga isasshen sabbi.

Yan Najeriya na kwashe sa'o'i a layukan banku don samun kudi kuma duk da haka ba zasu iya fitar da sama da N20,000 ba.

Kara karanta wannan

Ba Dan Takarar da Zai Samu Kaso 70 a Arewa" Yakassai Ya Fadi Wanda Zai Gaje Buhari a 2023

Masana na ganin muddin wannan tsanani ya cigaba abin zai kai mutane bango kuma hakan na iya zama matsala ga zaben.

Tuni ranar Alhamis matasa sun fara zanga-zanga a garin Ibadan.

Fusatattun matasan sun fasa ofishin gwamna da bankin Wema.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa a bashi kwanaki bakwai zai magance matsalar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel