Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen Tinubu/Shettima Ke Gudana Yau A Lafiyan Bare-Bari

Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen Tinubu/Shettima Ke Gudana Yau A Lafiyan Bare-Bari

Kwamitin kamfen takarar kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyyar All Progressives Congree APC ta shiga jihar Nasarawa, a yau Asabar, 4 ga watan Febrairu, 2023.

Dan takarar shugaban kasan APC, Asiwaju Bola Tinubu; abokin tafiyarsa, Kashin Shettima; shugaban uwar jam'iyyar, Abdullahi Adamu da sauran jiga-jigai sun dira Lafiya.

Jawaban Shugaba Muhammadu Buhari

"Ina tabbatar muku zamu yi nasara. Na san Bola Tinubu tsawon shekaru 20 da suka wuce.
Zan cigaba da yiwa Bola Tinubu kamfe. Dan Najeriya ne na gaskiya kuma zai yi iyakan kokarinsa ga Najeriya.
Ku zabi Ahmed Bola Tinubu, Ya yarda da Najeriya. Yana kaunar wannan kasa. Zai yi duk abinda zai taimakemu gaba daya. Saboda Allah, ku kaya abokanku da iyalanku su sa mishi kuri'a. Dukkanmu zamu zabo Bola Tinubu."

Bola Tinubu ya fara jawabi

"A yau na tsaya gabanku ina muku alkawarin cewa Najeriya zata kawar da dukkan wadannan kalubale, mu jajirtattu ne, zamu mayar d ahankali kan aikin noma, zamu hako ma'adinan kasa,
Muna muku alkawari 'yayanku da jikokinku ba zasuyi nadama ba.

Buhari ya samar da arzikin mai a jihar Nasarawa

Shugaban uwar jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa al'ummar jihar Nasarawa su godewa shugaba Muhammadu Buhari saboda hakar arzikin mai a jihar.

Adamu ya ce nan da yan kwanaki za'a fara hakar danyen mai a karamar hukumar Keana a jihar.

Shugaban na APC ya baiwa al'ummar hakuri bisa wahalar man fetur da ake yi da kuma karancin takardun Naira.

Ya jaddada godiyarsa ga shugaba Buhari saboda shi dan jihar Nasarawa be.

Haka ya gode bisa ba shi kujerar shugabancin APC.

Shugaba Buhari ya dira farfajiyar taro

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira farfajiyar taron kamfen jam'iyyar APC a jihar.

Online view pixel