ICPC Ta Kwamushe Manajan Bankin da Ya Daure Sabbin Naira a Cikin Na’urar ATM
- Hukumar ICPC a jihar Osun ta yi nasarar kame wani manajan banki da ke haramtawa ‘yan Najeriya sabbin Najeriya
- An gano daurin sabbin kudade a makare a cikin injunan ATM, amma an daure su ta yadda ba za a iya cire kudin ba ko ta halin kaka
- ‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar tashin hankali game da lamarin da ya shafi sabbin kudi, musamman bayan kara wa’adi
Osogbo, jihar Osun - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta kama wani manajan banki a birnin Osogbo a jihar Osun bisa zargin yana hana mutane samun sabbin Naira.
A cewar rahoton da muka samo daga hukumar, manajan bankin na daure sabbin kudaden a lokacin da zai saka su cikin injunan ATM, wanda hakan ke hana kudin fita kwata-kwata.
Wannan na zuwa ne daga bayanan da hukumar ta ICPC ta yada a shafinta na Twitter a ranar Juma’a 3 ga watan Fabrairun 2023.
A cewarta, a lokacin daka gano hakan, nan take jami’an hukumar suka umarci a gyara yadda ake saka kudin tare da barin kowa ya cire cikin tsanaki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yadda manaja ya shiga hannun ICPC
Sanarwar hukumar ta ce:
“Tawagar ICPC a Osogbo ta bankado bankin FCMB na Osogbo, jihar Osun inda aka cika wasu injunan ATM da kudaden da ke daure ba tare da ware su ba, don haka kudin ba sa fita daga injunan.
‘Saboda haka tawagar ta umarci a kunce dukkan daurukan kudin, kuma a daidaita yadda ake saka kudin.
“Sai dai, da aka bi diddigi a wata ziyarar duba a washegari don tabbatar da bin umarnin. Tagawar ta tarar injunan ATM din na makare da daurarrun kudade. An kama manajan bankin kuma ana bincikarsa.”
‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar tashin hankali da rikici game da sabbin kudin da aka buga kasancewar ba sa samunsu a bankuna.
A kan talaka wahalar sabbin Naira zai kare
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kaduna ya ce akwai gwamnan da ya cire zunzurutun kudi N500m daga banki na sabbin Naira.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake kira ga gwamnatin Buhari da ta duba kara wa’adin daina amfani da tsoffin kudi.
‘Yan Najeriya na ci gaba da kuka da halin da ake ciki na karancin sabbin kudi, El-Rufai ya ce hakan zai shafi tattalin arzikin kasa.
Asali: Legit.ng