Kotun Koli Ta Sake Tabbatar da Laila Buhari a Matsayin ’Yar Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya a PDP
- Rahoton da muke samu daga babban birnin tarayya Abuja ya bayyana cewa, kotun koli ta tabbatar da takarar Laila Buhari
- A baya kotun daukaka kara ya tabbatar da Laila a matsayin wacce za ta rike tutar PDP a zaben sanatan bana na Kano ta tsakiya
- A bangare guda, kotu ta kori dan takarar gwamnan APC a jihar Taraba bayan kai ruwa rana a kotu har uku
FCT, Abuja - Kotun koli a ranar Alhamis ta sake tabbatar da Hajia Laila Buhari a matsayin ‘yar takarar sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar PDP a zaben bana, inji Solace Base ta ruwaito.
An ruwaito cewa, a baya kotun daukaka kara ta tabbatar da Laila, inda ta soke zaban Danburam Nuhu a matsayin dan takarar mazabar na PDP.
Babbar kotun a hukuncin da ta yi karkashin jagorancin Muhammad Lawal Garba ta yi watsi da dukkan hujjojin da wanda ya daukaka karar, Danburam ya gabatar a gabanta.
Sauran alkalan da suka ciyar da Danburam taliyar karshe a hukuncin sun hada da Kudirat Kekere Ekun, Saulawa, Ibrahim Jauro da Emmanuel Etim.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda batun ya faro
A tun farko, jam’iyyar PDP ta kalubalanci hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke kan soke zaban Danburam, inda ta runtuma zuwa kotun koli, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ta nemi kotun koli da ta duba tare da yin watsi da hukuncin kotun daukaka kara tare da ayyana Danburam a matsayin sahihin dan takarar da zai taka a zaben 2023.
Sai dai, reshe ya juya da mujiya, aka samu akasin haka, inda alkalai biyar na kotun kolin suka bayyana rashin gamsuwarsu da hujjojin jam’iyyar PDP.
Yanzu-Yanzu: Murna A Yayin Da Kotu Ta Bada Hukuncin Karshe Kan Shari'ar Gwamnan PDP Mai Karfi A Babban Jihar Kudu
Hakazalika, sun caccaki PDP tare da yiwa jam’iyyar gargadi kan mummunan dabi’ar nuna son kai da wariya a lamurran da suka shafi siyasa.
A yanzu dai kwanaki kadan ne suka rage a yi zaben sanata a Najeriya, kuma laila ce wacce za ta taka rike da tutat PDP a akwatin sanatan mazabar Kano ta tsakiya.
An kwace tikitin dan takarar gwamnan APC a Taraba
A wani labarin kuma, dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar Taraba ya rasa tikitin takarar gwamnan jihar da aka ce ya lashe a zaben fidda gwani.
Alkalan kotun koli ne suka yanke hukunci bayan lura da hujjojin da suka zo gaban kotu bayan hukuncin kotun daukaka kara da na tarayya.
Wannan batu dai na zuwa ne yayin da ya saura kwanaki kadan a babban zabe a Najeriya, an bayyana wanda ya yi nasara.
Asali: Legit.ng