Yadda Rashin Sabbin Kudi Ya Yi Sanadiyar Rasa Ran Wata Mai Juna Biyu a Kaduna

Yadda Rashin Sabbin Kudi Ya Yi Sanadiyar Rasa Ran Wata Mai Juna Biyu a Kaduna

  • Wani magidanci ya sharbi kuka yayin da ya bayyana yadda ya rasa matarsa a sanadiyyar rashin wadatattun kudi
  • Wannan lamari ya faru ne a jihar Kaduna, inda ya kai matarsa asibiti amma ya rasa kudin da zai bayar don mata jinya
  • 'Yan Najeriya na ci gaba da shiga tasku saboda karancin sabbin kudi da aka buga a kwanakin baya a kasar

Kajuru, Kaduna - Wata mata tsohon ciki a kasuwar Magani a kamar hukumar Kajuru ta rasa ranta saboda karancin sabbin Naira da ake fama dashi a kasar nan.

Wannan ya faru ne sakamon yadda mijinta ya nemi sabbin kudi a banki domin biyan kudin jinya a asibiti amma ya gaza samun kudi a cikin banki, Tribune Online ta ruwaito.

James Auta, mijin matar da ta mutu ya ce, an ki karbar matarsa a asibiti lokacin da ya gaza biyan kudi nakadan saboda karancin sabbin kudade da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Toh fa: Ba a isa a hana mu sabbin kudi ba, talaka ne mai shan wahala, inji Kwankwaso

Yadda karancin sabbin Naira ya kai ga mutuwar wata mata a Kaduna
Yadda Rashin Sabbin Kudi Ya Yi Sanadiyar Rasa Ran Wata Mai Juna Biyu a Kaduna | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Na gaggauta zuwa bankina domin cire kudi amma aka ce min babu kudi. Na fita neman masu POS, amma ban samu ba saboda, tunda aka fara batun sabbin kudi, da yawa sun rufe shagunansu.”

Ya shaida cewa, ganin ba zai iya samun kudi ba, sai shi da matar suka yanke su koma gida su dangana da fatan Allah ya sauke ta lafiya.

An yi rashin sa'a, matarsa ta rasu

Sai dai, an yi rashin sa’a, jikinta ya yi tsanani wanda Allah ya dauke kayansa a lokacin da take kokarin haihuwa, Tori ta tattaro.

James ya tuna da cewa:

“Matata ta fara nakuda tun kusan 11 na dare. Tunda ba zan iya cire kudi ba, na kira wata unguzoma a unguwarmu. Amma lokacin da matata ta haihu, jini ya ki tsayawa. Dukkan kokarin da unguzomar ta yi na tsayar da jinin ya gagara.”

Kara karanta wannan

Samun wuri: Matar da ta gawurta wajen siyar da Nara ta kare a hannun ICPC, an gano masu bata kudi

Talaka ne batun sabbin kudi zai cuta, ba 'yan siyasa ba, cewae Kwankwaso

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP ya bayyana kadan daga abin da yake gani kan batun sauya kudin kasa.

Ya ce, babu bankin da zai hana dan takarar shugaban kasa kudi, saboda 'yan siyasa ne ke da ragamar kasar nan.

Kwankwaso ya kuma bayyana cewa, ya kamata a duba tare da sassautawa talakawan Najeriya kan batun kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.