Najeriya ta Fada Makoki Bayan Fitaccen Tsohon Gwamna a Arewa ya Rasu

Najeriya ta Fada Makoki Bayan Fitaccen Tsohon Gwamna a Arewa ya Rasu

  • Tsohon gwamnan soji, Commodore Dan Suleiman ya kwanta dama ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu, 2023 yana da shekaru 81
  • Suleiman, wanda tsohon gwamnan jihar Filato ne, na daya daga cikin wadanda suka kafa hukumar dimakaradiyya ta kasa (NADECO)
  • Haka zalika, tsohon 'dan siyasan na daya daga cikin wadanda suka tsaya tsayin daka don samar da hukumar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS)

Dan Suleiman, daya daga cikin wadanda suka samar da Kungiyar Dimakaradiyya ta Kasa (NADECO) ya kwanta dama.

Tsohon gwamnan jihar Fulato, Dan Suleiman ya rasu yana da shekaru 81 a ranar Laraba, 1 ga watan Fabrairu.

Dan Suleiman ya taka mihimmiyar rawa wajen kafa hukumar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), inda ya yi aiki a matsayin Kwamishinan ayyuka na musamman a gwamnatin Janar Yakubu Gowon.

Kara karanta wannan

Kada ku sake kara wa'adin daina amfani da Naira, Atiku ga CBN

Dan Sulaiman
Najeriya ta Fada Makoki Bayan Fitaccen Tsohon Gwamna a Arewa ya Rasu. Hoto daga tribuneonline.ng
Asali: UGC

A wata takarda da ta tabbatar da rasuwar Suleiman, Opadokun ya siffanta tsohon gwamnan a matsayin:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jajirtacce, mai kwazo, mai kishin kasa, mai tsan-tsar burin cigaban kasa, wanda rayuwarsa da lokacinsa ya ke amfani dasu don abubuwa kwarai da bautawa Ubangiji da al'umma."

Takardar ta bayyana:

"Hukumar Dimokaradiyya ta Kasa (NADECO) na son sanarwa cike da alhini da mutuwar ba-zatar daya daga cikin wadanda suka kafa mu, kuma jigo, Commodore Dan Suleiman.
"Dan Suleiman mutumin kwarai ne, jajirtacce kuma shugaba mai adalci wanda kyawawan halayensa zai yi wahala a iya zayyanosu duka. A ina zamu sake samun wanda zai maye mana gurbin Dan Suleiman?
"Bayan juyin mulkin janar Gowon da janar Murtala Muhammad ya yi, an sake nada Dan Suleiman a matsayin Kwamishinan Lafiya.
"Na uku, yayin da janar Babangida ya soke zaben da MKO Abiola ya lashe na shugaban kasa a 1993, janar Abacha daga bisani ya kafa kwamitinsa na kula da kasa, Suleiman ya kalubanta gami da kin amincewa da soke zaben."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Hadimar Gwamna Tambuwal Ta Mutu Sakamakon Cinkoso Lokacin Kamfen Atiku a Sokoto

Dandazon jama'a sun halarci jana'izar Sarkin Dutse

A wani labari na daban, dubban jama'a da suka hada da Sarakuna, hamshakan masu arziki, 'yan siyasa da masu fadi a ji sun halarci jana'izar marigayi mai martaba, Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi, Sarkin Dutse a jihar Jigawa.

Marigayin ya kwanta dama yana da shekaru 79 a duniya bayan gajeryar rashin lafiya da yayi fama da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: