Da ɗumi-ɗumi: Daga Karshe, Kotu ta raba auren Hajiya Asiya Ganduje da Mijinta

Da ɗumi-ɗumi: Daga Karshe, Kotu ta raba auren Hajiya Asiya Ganduje da Mijinta

  • Bayan mako da makonni, an kawo karshen zaman shari'a tsakanin diyar gwamnan Kano da mijinta
  • Asiya Ganduje ta bukacir kotu ta raba aurenta da Alhaji Inuwa Uba saboda ta gaji da zama da shi
  • Mijin Alhaji Inuwa Uba ya lissafa wasu abubuwa da yake son tayi masa idan tana son ya amince a raba auren

Kano - Labarin dake shigowa da duminsa nan Kotu ta datse igiyar auren Hajiya Asiya Balaraba Ganduje.

Freedom Radio ya ruwaito cewa Alkalin kotun ya amince da bukatar Khul’in Asiya Ganduje.

Alhaji Inuwa Uba da Asiya Ganduje sun kwashe shekaru goma sha shida da aure gabanin wannan matsala.

Ta nemi a raba auren saboda ta gaji da zama da shi kuma tabi ta hanyar khul'i.

Asiya
Da ɗumi-ɗumi: Daga Karshe, Kotu ta raba auren Hajiya Asiya Ganduje da Mijinta
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan Sanda Na Neman Wani Mutum Ruwa A Jallo Saboda 'Bidiyon Bindiga' A Legas

Rahoto ya nuna cewa Asiya Ganduje ta mayar da kudin sadaki N50,000 da mijin ya biya lokacin da aka daura aurensu.

Takkadama tsakanin Aisya da MIjinta

Kwanakin baya a kotu Alhaji Inuwa Uba ya laburtawa Alkali cewa matarsa ta kwashe masa wasu dukiya dake gidan da suke zama.

Ya tuhumi Asiya Ganduje ta fasa gidan ta dauke wasu muhimman takardun filaye, motoci da mukullai.

Yace yana son a yi sulhu amma ta kiya.

A cewarsa:

"Akwai 'yaya hudu da ta haifa masa amma duk yunkurin sulhun da aka yi ya ci tura."

Lauyan mijin Umar I. Umar, ya bayyanawa kotu cewa wanda yake wakilta na da sharruda biyu game da wasu dukiyoyinsa,

Ya ce Idan tana son a raba auren ta dawo da dukkan takardunsa, takardun gidajensa, motoci, da hannun jarin da take da shi a kamfanin shinkafarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel