Kungiyoyin Musulumi A Najeriya Sun Koka Kan Hana Amfani Da Hijabi

Kungiyoyin Musulumi A Najeriya Sun Koka Kan Hana Amfani Da Hijabi

  • Kungiyoyin musulmi da dama a Jihar Lagos sun yi kira da a daina cin zarafin mata saboda sanya hijabi
  • Kungiyoyin a sunyi kiran ne a matsayin wani sashe na bikin tunawa da ranar hijabi ta duniya da ta gudana jiya
  • Kungiyoyin sun kuma ce hijabi hakki ne akan mata musulmi kuma bai kamata ya zama abin kyama a wajen mutane ba

Legas - Kungiyoyin musulmi a Najeriya sun yi gargadi kan alakanta sanya hijabi da laifi sun kuma bukaci da a kalli hakan a matsayin mutunta addinin su. Sun yi kiran ne a jiya don bikin tunawa da ranar Hijabi ta duniya.

Kungiyoyin su kuma nuna jin dadin su da hukuncin kotun koli kan batun hijabin ta kuma yi kira ga jihohin da basu bi hukuncin ba da su cika umarnin kotun, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Rudani: 'Yan Najeriya sun fusata, sun fara zanga-zanga sabuwa karancin sabbin Naira

Hijabi
Kungiyar Musulumi A Najeriya Sun Koka Kan Hana Amfani Da Hijabi. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

Kungiyoyin da suka yi kiran sun hada da kungiyar mata musulmi na tarayyar Najeriya (FOMWAN Lagos), kungiyar masu kare hakin hijabi (Hijab Rights Advocacy Initiative), kungiyar dalibai musulmi MSSN reshen Jihar Lagos, kungiyar The Criterion, kungiyar Nasrul-lahi-li Fathi (NASFAT), Al Muminaat: kungiyar mata musulmi, cibiyar hulda da jama'a kan al'amuran musulmi (MPAC), MURIC da sauran gidauniyar Pristine Cactus.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran sun da kungiyar mata musulmi ta kasa da kasa (IMWU), gidauniyar Pure heart Islamic Foundation (PHF Lagos), Muslim Media practitioners of Nigeria, Islamic Medical association of Nigeria (IMAN), Akhawat, Izarul Haq, LSCCM da kuma kungiyar mata ta An-Nujabau.

Shugabar taron kuma babbar daraktar HRAI, Mutiat Oruka-Balogun, ta ce kungiyar na yaki da cin zarafin hijabi a fadin duniya, nuna wariya da kuma kuntatawa mata musulmi saboda gudunar da abin da addinin su ya hukunta.

Kara karanta wannan

Samun wuri: Matar da ta gawurta wajen siyar da Nara ta kare a hannun ICPC, an gano masu bata kudi

A cewarta:

''An kafa WHD shekaru 11 baya kuma yanzu akwai reshe a kasashe 190 a fadin duniya.''

Ta ce taken bikin na bana 'cigaba ba kunci ba', zai tunawa mutane cewa sanya hijabi doka ne mai hukunci ga matan musulmi sama da shekaru 1,400 da suka gabata.

Shugabar FOMWAN reshen Jihar Lagos, Alhaja Sherifat Ajagbe, tayi kira da gwamnati da ta kare mata daga irin cin zarafin da ake yi musu a fadin kasar nan.

Mata sun yi zanga-zangan nun adawa da hijabi, sun cinnawa lullubi wuta a Iran

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mata a Iran sun yi zanga-zangan nuna kin jinin saka hijabi bayan mutuwar wata mata da aka tsare.

An tsare matar ne kan zargin saba dokar sanya hijabi a yankin Sari da ke kasar Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164