Bidiyon Yadda ’Yan Najeriya Ke Zanga-Zanga a Gaban Bankunan Kasar Kan Karancin Sabbin Naira
- ‘Yan Najeriya sun shirya wata zanga-zanga a hedkwatan bankunan kasar game da karancin sabbin Naira
- Sun nuna rashin jin dadinsu ga bankuna da babban bankin Najeriya (CBN) game da sabbin ka’idojin sabbin kudi
- Tun bayan da aka samu karancin kudi a Najeriya, masu POS suka kara adadin kudaden da suke caji wajen cire tsabar kudi
Wasu gungun mutane a jihar Legas sun shirya wata zanga-zanga a hedkwatan bankunan aksuwanci da yawa a birnin Legas.
A wani bidiyin da aka yada a kafar sada zumunta, ‘yan zanga-zangan sun zargi bankuna da kin bin ka’idar CBN game da sabbin kudi, lamarin da ya ke ba talakawan kasar wahala.
An shirya wannan zanga-zanga ne karkashin kungiyar farar hula ta Coalition of Civil Society Organizations for Good Governance, (CCSGG), Leadership ta ruwaito.
A lokacin zanga-zangar, kungiyar ta yi kira ga bankuna da su saki sabbin Naira ga kowa a Najeriya don ci gaba da harka yadda aka saba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kungiyar CCSGG ta zargi bankuna da shirya manakisa
Etuk Williams Basseyed, shugaban kungiyar CCSGG ne ya jagoranci zanga-zangar, kuma ya bayyana rashin jin dadinsa ga yadda bankuna ke mua’amalantar kwastomomi a kasar nan game da ka’idojin sabbin kudi na CBN.
Bassey ya bayyana cewa, kungiyar ta dauki kudurin tallafawa CBN wajen tabbatar da ka’idojin kudi da babban bankin ya sanya.
Ya ce:
“Mun taru a nan ne a yau don nuna cikakken goyon bayanmu ga gwamnan CBN da shugaba Buhari game da ka’idar sabbin kudi da ta zo.
“Tun lokacin da aka gabatar da sabbin kudi muke ganin wasu cin dunduniya da ke aiki don ganin an lalata dokar ta hanyoyi da yawa don bata lamarin.
“Muna godiya ga tsayin daka ba gwamnan CBN tare da taimakon shugaban kasa game da dokar.
“A rubuce yake rabonmu da yin irin wannan doka shekaru 19 kenan da suka gabata, kuma an samu damar yin haka ne ta hanyar tsayayyen shugaba ta hanyar misali daga gwamnan CBN tare da taimakon shugaban kasa.”
Shugaban na CCSGG ya bayyana cewa, kungiyar za ta sanya ido kan hada-hadar bankunan don tabbatar da suna bin ka’idojin da CBN ta shar’anta game da sabbin kudi.
Kalli bidiyon yadda ake fama da bankuna game da sabbin kudi
A nan kuma, wani kwastoma ne a Najeriya da ya kutsa kai babban bankin Najeriya watakila don bayyana kokensa game da sabbin kudi.
A bangare guda, masu POS suna ci gaba da tsawwalawa 'yan Najeriya wurin cajinsu kudade masu a wurin cire kudi.
A irin haka ne hukumar ICPC ta kwamushe wata mata da ke tallan kudi a kafar Twitter a yayin da ake bukatar sabbin Naira.
Hukumar ta bayyana yadda ta kai ga kame matar da ke harkallarta a kafar sada zumunta.
Asali: Legit.ng