Babu Wani Banki da Zai Hana ’Yan Siyasa Kasa Kudi, CBN Kawai Talakawa Yake Ba Wahala, Kwankwaso
- Dan takarar shugaban kasa a NNPP ya bayyana kadan daga rikicin da ke tattare da batun sauyin sabbin kudi
- Kwankwaso ya ce manyan kasar nan ne masu bankuna, don haka babu abin da zai hana su samun sabbin kudi
- 'Yan Najeriya na ci gaba da samun tsaiko wajen samun sabbin kudaden da aka buga a kwanakin nan
Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, sabbin ka’idojin kudi na CBN da ke ganin zai shafi ‘yan siyasa ba komai bane face bata lokaci.
Kwankwaso ya ce, manyan ‘yan siyasa, kamar ‘yan takarar shugaban kasa ko da sun mallaki banki ko kuma suna da wani kaso mai tsoka a bankunan ko kuma abokansu ne masu bankunan a kasar nan.
Ya bayyana cewa, duk wani adadi na kudi da suke bukata za su samu kasancewar su ke da su ba kowa ba a kasar nan.
Babu bankin da zai hana 'yan takarar shugaban kasa sabbin kudi
Ya kuma bayyana cewa, babu wani banki da ke aiki a Najeriya da ke ikon hana dan siyasa kudi, kawai duk wahalar da ake ciki a kan talaka zai kare.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwankwaso ya bayyana wadannan maganganu ne a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis 2 ga watan Fabrairun 2023.
Ya ce:
"Me zai sa Najeriya ta kakaba irin wannan kunci ga mutanen da dama ke fama da wahala."
Ya kamata CBN ta ba da wadataccen lokaci
Kwankwaso ya bayyana bukatar CBN ta ba da wadataccen wa'adi da zai ba kasa aiwatar da wannan manufa cikin tsanaki kuma mataki-mataki.
A bangare guda, tattaunawar da aka yi Kwankwaso ta tabo tafiyar siyasarsa da kuma batun tattaunawarsa da sauran jam'iyyun siyasa a kasar.
A wani labarin kuma, kunji yadda hukumar ICPC mai yaki da rashawa a Najeriya ta kama wata mata da ke harkallar sabbin Naira a kafar Twitter.
An gano matar na tallar kudi sabbi a Twitter, tare da cajin wani adadi da ya saba ka'ida da hakascin musayar kudu a Najeriya.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da 'yan Najeriya ke ci gaba da shiga damuwa game da karancin sabbin Naira.
Asali: Legit.ng