‘Duk da Ya Maido Naira Biliyan 6.9’, EFCC Za Tayi Shari’a da Tsohon Akanta Janar
- Kotun daukaka kara ta rusa gaskiyar da Mai shari’a I.E. Ekwo ya ba Jonah Otunla a kotun tarayya
- Alkalan babban kotun sun ce babu hujjar da za ta haramtawa EFCC binciken sohon Akanta Janar din
- Jonah Otunla ya kafe da cewa an yi alkawarin za a yafe masa idan ya dawo da abin da ke hannunsa
Abuja - Kotun daukaka kara ta watsar da hukuncin da aka zartar a baya, wanda ya haramtawa hukumar EFCC binciken tsohon AGF, Jonah Otunla.
The Cable ta ce Alkalai uku su ka saurari shari’ar Jonah Otunla a kotun daukaka kara, a karshe aka ce ya gaza kawo takardar yarjejeniyarsa da EFCC.
Danlami Senchi da ya karanto hukuncin ya ce kotu ba za tayi amfani da maganar fatar baki, sai ta zartar da cewa ba za a binciki tsohon jami'in ba.
“A wannan yanayi, babu wata hujjar da ke nuna cewa ba za a binciki wanda ake kara (Otunla) da laifi ba ko kuma a fasa yin shari’a da shi.
Babu wata shaida a takarda da ke nuna sulhu da kwamitin shugaban kasa mai gano dukiyoyin sata.
A karshe, kotun daukaka kara ta bada dama ayi bincike, an jinginar da shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/2321/2021 da kotun tarayya ta yi.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Danlami Senchi
Jaridar ta ce a Yulin 2021, I.E. Ekwo ya zartar da cewa ba za ayi shari’a da Otunla a kotu ba.
Yadda muka yi da Magu - Otunla
Tsohon Akanta Janar din ya yi ikirarin a lokacin Ibrahim Magu yana rike da EFCC, ya yi masa alkawarin za a yafe masa idan ya dawo da abin da ya dauka.
Daily Nigerian ta ce ana binciken Jonah Otunla da zargin karkatar da N24bn da ya kamata a biya ma’aikatan kamfanin PHCN da aka kora daga aikinsu.
Sannan ana zargin shi da laifin karbar N2bn daga ofishin NSA. Daga baya an rahoto cewa ya dawo da wasu kudi da ke hannunsa domin yafe masa laifinsa.
Umarnin NSA na bi - Obanikoro
A wani rahoto da muka fitar dazu, kun ji cewa Musiliu Obanikoro ya bada shaida a shari’ar tsohon Gwamnan Ekiti watau Ayo Fayose da Hukumar EFCC.
Watakila tsohon Ministan tsaron ya jefa Kanal Sambo Dasuki a matsala a bayanan da ya yi domin ya ce tsohon NSA din ne ya umarce shi ya fitar da N1.2bn.
Asali: Legit.ng