Abubuwa Sun Lafa, APC Ta Fadi Wadanda Suka Kai wa Tawagar Buhari Hari a Kano

Abubuwa Sun Lafa, APC Ta Fadi Wadanda Suka Kai wa Tawagar Buhari Hari a Kano

  • Jam’iyyar APC ta ce ba kowa suka kai wa Muhammadu Buhari hari a Kano ba illa ‘Yan PDP
  • Felix Morka yake cewa Jam’iyyar PDP ta tona kan ta da kan ta da kalaman Debo Ologunagba
  • Ologunagba ya yi Allah-wadai da abin da ya faru, amma APC ta ce PDP ta tonawa kanta asiri

Kano - Jam’iyyar APC ta zargi ‘yan PDP da hannu a harin da ake zargin an kai wa tawagar shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya ziyarci Garin Kano.

A wani rahoto da The Cable ta fitar ranar Laraba, an ji cewa APC tana tuhumar jam’iyyar PDP da kitsa harin da aka kai wa Mai girma Muhammadu Buhari.

A jawabin da ta fitar, PDP ta yi Allah-wadai da wannan mummunan aiki da wasu suka yi. Mista Debo Ologunagba ya kamanta hakan da cin amanar kasa.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Kuma Sukar Mulkin Shugaba Buhari a Gaban Jama’a Wajen Yawon Kamfe

Kakakin babbar jam’iyyar adawar, Ologunagba ya ce kyau kowa ya yi tir da abin da ya auku.

Ahaf, aikin 'Yan PDP ne - APC

Amma mai magana da yawun bakin jam’iyyar APC na kasa, Felix Morka ya ce kalaman da suka fito daga bakin PDP ya nuna su ke da hannu a harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An rahoto Felix Morka yana jifan ‘yan jam’iyyar PDP da dauko hayar mutanen da za su ci mutuncin shugaban kasa, ya ce adawarsu ta zama bakar siyasa.

Shugaban kasa
Shugaban kasa ya ziyarci Kano Hoto: @MuazuJajiSambo
Asali: Twitter

Farin jinin Buhari zai shafi Tinubu

Kakakin APC na kasa yake cewa ba za su yarda da wannan ba, sannan ya bukaci jami’an tsaro su gudanar da bincike domin a cafke wadanda suka yi laifin.

Morka yake cewa jam’iyyar hamayyar ta tsorata da irin kyakkyawar alaka da dankon da ke tsakanin shugaban kasa da ‘dan takaranta watau Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Miyagu Sun Sace Darektan Yakin Neman Zaben Jam’iyyar APC a Wajen Yawon Kamfe

APC ta ce kaunar da talakawa suke yi wa Buhari za ta rabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zabe.

Leadership ta rahoto Sakataren yada labaran na jam’iyya mai mulki yana kira ga jama’a su zabi Tinubu, ya ce shi ya fi cancanta ya karbi shugabanci a 2023.

Kotu ta sa a cafke shugaban APC na Kano

Abdullahi Abbas wanda ya saba cewa ko da tsiya-tsiya sai APC ta ci zabe a Kano ya shiga uku bayan an ji labari wani mutumi ya ce ya yi barazanar kashe shi.

A dalilin haka aka kai kara kotu, kuma aka yi umarni a cafke shugaban na APC. Jam'iyyar NNPP tayi murnar jin hukuncin da aka zartar a kotun na tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng