Masu Son Hada Buhari Fada Da Tinubu Ba Zasu Yi Nasara ba: Fadar Shugaban Kasa

Masu Son Hada Buhari Fada Da Tinubu Ba Zasu Yi Nasara ba: Fadar Shugaban Kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa yunkurin da yan adawa ke yi na hada rigima tsakanin Shugaba Buhari da dan takaran shugaban kasan APC, Asiwaju Bola Tinubu, ba zai basu nasara ba.

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa da ya fitar da jawabi ya ce jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, su mayar da hankali kan kamfensu, rahoton Vanguard.

An shiga watan zabe kuma saura kwanaki 24 kacal zaben shugaban kasa.

Buhari
Masu Son Hada Buhari Fada Da Tinubu Ba Zasu Yi Nasara ba: Fadar Shugaban Kasa Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Garba Shehu ya ce labarin da PDP ke yadawa cewa an yiwa shugaba Buhari jifar shaidan a Kano ba gaskiya bane ko kadan.

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mun ga rahotannin boge cewa an jefi shugaba Muhammadu Buhari a unguwar Hotori na jihar Kano ranar Litinin inda ya kai ziyara. Komin kankantar wannan abu, ya cancanci abin Alla-wadai."

Kara karanta wannan

2023: Wasu Masu Son Gaje Buhari Abin Dariya Ne, Gwamnan Arewa Ya Tabo 'Yan Takarar Shugaban Kasa

"Yunkurin da yan adawa ke yi na kokarin bata sunan shugaban kasa da yan takaran jam'iyyar APC a zabe mai zuwa, kuma su sani kokarin da suke yi na haddasa rabuwar kai tsakanin jam'iyyar da gwamnati ba zai basu nasara (a zabe) ba."
"Jam'iyyar adawar dake da jihohi 14 amma za ta shiga zabe da jihohi takwas ko tara kamata yayi ta duba dalilin barakar cikin gidanta da kamfenta mara karko."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida