Gwamnan CBN Makiyin Dimokradiyya ne, Jigon APC Kayode ya Kunto kura game Da Sabbin Naira

Gwamnan CBN Makiyin Dimokradiyya ne, Jigon APC Kayode ya Kunto kura game Da Sabbin Naira

  • Jigon APC kuma mai tallata Tinubu ya yiwa CBN barin makauniya, ya caccaki gwamnan bankin kan batun sabbin Naira
  • Femi Fani Kayode ya ce, gwamnan CBN na da mugun nufi game da sabbin kudi akan ‘yan Najeriya a wannan lokacin
  • A baya Tinubu ya caccaki CBN da gwamnatin Najeriya game da batun sauya fasalin kudi da kuma karancin man fetur a kasar

Baya ga yadda dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmad Tinubu ya zargi CBN da wasu tsirarun mutane da kawo batun sauyin kudi don bata siyasarsa, wani batu ya fito daga na hannun damansa.

Femi Fani Kayode, daraktan gangamin kamfen Tinubu a APC ya sake sakin wata magana mai girma game da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, PM News ta ruwaito.

Idan baku manta ba, a watan Disamban bara ne babban bankin Najeriya ya sanar da sake fasalin Naira tare da kawo sabbi don habaka tattalin arziki da kuma magance matsalar tsaron kasar.

Kara karanta wannan

Yadda ‘Yan ‘Yahoo Suka Damfari Tsohuwa, Suka Sace Duka Dukiyar da ta Mallaka

Kayode ya kunce CBN game da sauyin Naira
Gwamnan CBN Makiyin Dimokradiyya ne, Jigon APC Kayode ya Kunto kura game Da Sabbin Naira | Hoto: Femi Fani-Kayode
Asali: Facebook

Daga kudaden da za a daina amfani dasu, akwai N200, N500 da N1,000, kuma an kaddamar da sabbin a watan na Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanya wa’adin daina amfani da kudaden zuwa 31 ga watan Janairu, kafin daga bisani ‘yan Najeriya su nuna damuwa, aka mayar 10 ga watan Fabrairu.

Mugun nufi ne da gwamnan CBN, inji Kayode

Da yake jawabi game da sauyin da aka samu, jigon siyasan APC ya hango matsala, ya ce manufar gwmanan CBN bata kyau game da wannan canji

A wata sanarwa da Kayode ya fitar a ranar Talata 31 Janairu, 2023, ya siffanta gwamnan na CBN da makiyin dimokradiyya, Daily Post ta tattaro.

Tsohon ministan ya bayyana cewa, Emefiele bai da wata manufa ta sakin wadatattun sabbin kudaden da CBN ya buga a nan kusa.

Ya kuma yi ikrarin cewa, gwamnan bai da wata manufa da ta wuce ya kuntatawa ‘yan Najeriya ta hanyar hana su sabbin kudin da kuma sanya musu damuwa.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Majalisa ta yi martani mai zafi bayan kara wa'adin kashe tsoffin kudi a Najeriya

Hakazalika, ya zargi akwai yiwuwar hannun wasu biyayyun ‘yan PDP da ke marawa Atiku Abubakar baya a batun sauya fasalin Naira da aka yi.

Tinubu ya zargi Buhari da CBN da kokarin bata siyasarsa

A wani labarin, kunji yadda dan takarar shugaban kasa na APC ya bayyana bacin ransa game da yadda CBN ya kawo sauyin kudi a kasar.

Tinubu ya bayyana cewa, ya gano an sauya kudi ne domin kawo tsaiko ga tafiyar siyasarsa da kuma zaben 2023 gaba daya.

Hakazalika, Tinubu ya ce, batun tsadar man fetur da karancinsa ma duk lamari ne da ke nuna kawo tsaiko ga zaben 2023 da ke tafe nan kusa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.