Tattalin Arzikin Najeriya Zai Habaka a Cikin Shekarar da Aka Shiga Ta 2023, Majalisar Dinkin Duniya

Tattalin Arzikin Najeriya Zai Habaka a Cikin Shekarar da Aka Shiga Ta 2023, Majalisar Dinkin Duniya

  • Majalisar dinkin duniya ta hango sauyi a tattalin arzikin Najeriya nan da watanni 12 masu zuwa na shekarar 2023
  • A cewarta, za a samu habaka a tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika, ciki kuwa har da Najeriya
  • 'Yan Najeriya sun sha bayyana kukansu game da tattalin arzikin kasar nan, ana kyautata zaton sauyi

Yayin da ake ci gaba da kuka a Najeriya game da tabarbarewar tattalin arziki, majalisar dinkin duniya ta yiwa kasar bushara mai kyau a shekarar 2023, BBC ta tattaro.

A cewarta, ta hango yadda tattalin arzikin Najeriya sai habaka ya kuma bunkasa da kashi uku cikin 100 a shekarar da ta fara kwanaki 30 da suka gabata.

Majalisar ta fitar da wata sanarwar da ke bayyana halin da kasashe za su shiga a shekarar 2023 ta fannin tattalin arziki, ciki kuwa har da Najeriya.

Kara karanta wannan

Babu Gwamnati da Zata Iya Shawo kan Dukkan Kalubalen Najeriya ita Daya, Shugaba Buhari

Tattalin arzikin Najeriya zai gyaru, in ji majalisar dinkin duniya
Tattalin Arzikin Najeriya Zai Habaka a Cikin Shekarar da Aka Shiga Ta 2023, Majalisar Dinkin Duniya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Da take bayyana dalilin da ka iya kaiwa ga habakar tattalin arzikin, majalisar ta ce, karancin wutar lantarki da hauhawar farashin kayayyaki na da matukar tasiri a fannin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubuwan da za su habaka tattalin arzikin Najeriya

A cewar rahoton, habakar kasuwanci, sana’o’i da sauran lamurran yau da kullum ne za su farfado da tattalin arzikin kasar.

Hhar ila yau, ba Najeriya kadai ba, kasashen Yammacin Afrika za su ga kari mai tsoka ga tattalin arzikinsu a shekarar ta 2023, rahoton Premium Times.

A bangare guda, rahoton ya ce, karuwar farashin kayayyaki zai taimakawa ‘yan safarar kayayyaki a duniya duk kuwa da cewa hakan na da wata matsalar.

Game da matsala, majalisar ta yi gargadin cewa, raguwar haba-haba da bukatar kaya ka zai iya haifar da kalubalen cinikayya a duniya.

Baku isa ku karya tattalin arzikin kasa ba, majalisa ga CBN

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ainihin mutanen da ke boye sabbin kudi, suna siyarwa a boye a Arewa

A wani labarin kuma, majalisar wakilai a Najeriya ta ce ba za ta bari wasu tsirarun mutane su kawo tsaiko ga tattalin arzikin kasar nan ba.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da babban bankin kasar ya sauya fasalin kudi kuma wa'adin daina amfani da tsoffi ke karatowa.

Ya zuwa yanzu dai 'yan Najeriya na ci gaba da kuka kan halin da ake ciki na karancin sabbin kudaden kasar da aka buga a watan jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.