Daga Wasan Buya, Bacci Ya Dauki Yaro, Ya Tsinci Kansa a Kasar Waje

Daga Wasan Buya, Bacci Ya Dauki Yaro, Ya Tsinci Kansa a Kasar Waje

  • Wani karamin yaro ya shiga kwantenar daukar kaya zuwa wasu kasashe a lokacin da yake wasan buya da abokansa domin boye musu
  • A garin wasan ne ya kwanta bacci ya dauke shi a ciki, bai farka ba sai da aka yi tafiyar mil 2,000 da dashi a kan teku
  • An yi nasarar ceto yaron da ya dauki kwanaki shida a kwantane, ruwan jikinsa ya kare, ya gaji ga kuma alamun shan wahala a jikinsa

Wani yaro mai shekaru 15 ya shiga kwantenar daukar kaya zuwa kasar waje a lokacin da yake wasan buya da wasu abokansa.

An gano shi ne bayan da ya yi tafiyar kwanaki shida, nesa da gida da kasarsa kamar yadda wani rahoto ya bayyana.

DailyMail ta ruwaito cewa, yaron mai suna Fahim ya yi wasan buya tare da abokansa a ranar 11 ga watan Janairu a garin Chittaging da ke Bangladesh amma ya makale a kwantena.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Matashi Dan Najeriya Ya Dau Zafi, Ya Yi Barazanar Tarwatsa Banki Yayin da Jami’an Tsaro Suka Hana Shi Shiga a Bidiyo

Ya kwanta bacci ya dauke shi, bai farka ba sai da aka yi tafiyar mil 2,000 dashi zuwa kasar Malesiya da ke nahiyar ta Asiya.

Matashi ya yi dogon zango, an kaishi wata kasa cikin rashin sani
Daga Wasan Buya, Bacci Ya Dauki Yaro, Ya Tsinci Kansa a Kasar Waje | Hoto: dailymail.co.uk
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda abin ya faru

An ruwaito cewa, an yi wannan tafiyar ne tare dashi cikin rashin sani bayan da aka rufe shi cikin kwantena ba a san yana ciki ba.

A ranar 17 ga watan Janairu, ma’aikatan tashar jirgin ruwan Malesiya da ‘yan sanda suka gano yaron bayan da wani ma’aikaci ya ji yana buga kwantenar ta ciki.

A cewar ministan cikin gida na kasar Datuk Seri Saifuddin Nasution Ismail ga kafar labarai ta Bernama:

“An yi imani cewa yaron ya shiga kwantenar ne, bacci ya dauke shi, sai ya tsinci kansa a nan.”

Ya nemi da abinci cikin gaggawa bayan gano shi

A bidiyon da aka yada a kafar Reddit, an ga yaron na tsala ihun neman abinci da ruwa a lokacin da ya fito a rude cikin matukar rudewa da damuwa.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matashi Hankali Tashe Yana Nadamar Son Kudinsa, Yace Kwanaki Kadan Suka Rage ya Mutu

Bayan haka ne aka dauke shi zuwa asibitin Tengku Ampuan Rahimah a kasar ta Malesia domin duba lafiyarsa.

Hukumomi dai a farko sun nuna damuwar cewa, watakila an yi safarar yaron ne daga kasar waje. Tuni an fara shirin mayar da Fahim kasarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.