Dakarun Soji Sun Murkushe Yan Ta’adda 32 da Babban Kwamanda Abu Illiya a Borno
- Sojojin Najeriya sun kawar da mayakan Boko Haram masu yawan gaske a yayin wani arangama da suka yi a jihar Borno
- Dakarun rundunar sojin sun halaka mayakan Boko Haram 32 ciki harda babban kwamanda, Abu Illiya
- Sojojin sun isa har sansanin yan ta'addan da ke karamar hukumar Konduga inda suka sha karfinsu da wuta
Borno - Dakarun rundunar sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai Tare da hadin gwiwar yan sa kai na CJTF sun murkushe mayakan kungiyar ta'addanci 32 a jihar Borno.
Hakazalika dakarun sojin sun kashe babban kwamandan Boko Haram, Abu Illiya a yayin wani samame da suka kai sansanin yan ta'addan da ke karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.
An yi musayar wuta tsakanin sojoji da yan ta'addan
An tattaro cewa dakarun sun cimma wannan nasarar ne a yayin wani zazzafan fatrol da suka kai wasu mabuyar Boko Haram a kauyukan Kayamari, Habasha da Yuwe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu majiyoyin tsaro sun bayyana ma Zagazola Makama cewa dakarun sun yi karo da yan ta'addan a yayin da suke fatrol a Yuwe wanda ya yi sanadiyar musayar wuta a tsakaninsu.
Majiyoyin sun bayyana cewa sojojin sun yi nasarar lallasa mayakan na Boko Haram yayin da sauran suna tsere saboda karfin wuta daga sojojin inda suka yi watsi da kayayyaki da makamansu.
Rundunar sun kuma lalata kekuna 50 da aka samo a mabuyar yan ta'addan.
Jim kadan bayan ya karbi ragamar aiki, Manjo Janar Ibrahim Ali, sabon kwamandan JTF da Operation Hadin Kai a a arewa maso gabas ya sha alwashin jajircewa wajen yaki da ta'addanci.
Ya bayyana cewa dole a hada hannu don ganin karshen ta'adanci a yankin arewa maso gabas, rahoton Vanguard.
Ku zabe ni don kawo sauyi a Najeriya, Obi ya roki al'ummar jihar Borno
A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya roki al'ummar jihar Borno da su ba shi dama ya sauya Najeriya ta yarda kowa zai kwankwadi romon dadi.
Obi wanda ya ziyarci jihar a ranar Asabar, 28 ga watan Janairu, inda ya ce ya yi wa al'ummar arewa tanadi na musamman a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng