Bayan Shekaru 20, Matashi Ya Ziyarci Tsohon Da Ke Ba Shi Alawa a Hanyarsa Ta Dawowa Daga Makaranta

Bayan Shekaru 20, Matashi Ya Ziyarci Tsohon Da Ke Ba Shi Alawa a Hanyarsa Ta Dawowa Daga Makaranta

  • Wani matashi dan Najeriya ya wallafa labarin wani tsoho wanda kan yi masa kyautar alawa a hanyarsa ta dawowa daga makaranta
  • Mutumin mai suna Kamo Sende ya ce shekaru 20 baya, mutumin wanda ya mallaki karamin shago ya masa kyautar alawa
  • Ya binciko inda tsohon yake a garin Gboko, jihar Benue sannan ya yi masa godiya a kan alkhairansa gare shi

Wani matashi dan Najeriya ya bazama neman wani tsohon kirki wanda ya nuna masa kauna a lokacin da yake karamin yaro.

Mutumin mai suna Kamo Sende ya ce shekaru 20 baya, yana dawowa daga makaranta sai ya buge wani dutse inda ya fasa jarkan ruwan mutumin.

Matashi da dattijo
Bayan Shekaru 20, Matashi Ya Ziyarci Tsohon Da Ke Ba Shi Alawa a Hanyarsa Ta Dawowa Daga Makaranta Hoto: Facebook/Kamo Sende.
Asali: Facebook

Maimakon ya rufe shi da fada ko ya kai kararsa wajen iyayensa, sai mutumin mai suna Baba Augu ya kira shi zuwa shagonsa sannan ya ba shi alawa.

Kara karanta wannan

Gwamna Sule: Jajiberin 'Dana Zai Rasu, Na Dinga Rarrashin Mahaifin da ya Rasa Yara 9 da Shanu 70 a Tashin Bam din Nasarawa

Labarin Baba Augu, dan Najeriyan da ke kyautatawa yara

Kamo ya ce mutumin bai yi fushi ba kan cewa ya fasa masa jarkansa, maimakon haka sai ya yi masa nasiha sannan ya bar shi ya tafi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi bayanin cewa sai ya zama dabi'ar mutumin ba shi kyaututtuka a duk sanda yake dawowa daga makaranta a wancan lokacin.

Kamo ya ce shagon mutumin na nan a Bays Garden, wani shahararren otel a Gboko, jihar Benue. Ya yi wata wallafa game da Baba Augu kwanaki a Facebook kuma aka ce har yanzu yana tafiyar da karamin shagonsa.

Abokin Kamo, Siki Jnr Silas ya ziyarci tsohon a madadinsa. Hotuna masu tsuma zuciya da aka wallafa a Facebook ya nuno mutumin yana karbar wata kyauta a takardar anbulan.

Legit.ng ta tuntubi Kamo kuma ya ce ya aika wasu yan kudade ga Baba Augu. Ya ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon Matashi Hankali Tashe Yana Nadamar Son Kudinsa, Yace Kwanaki Kadan Suka Rage ya Mutu

"Eh. Na aika masa kudi kuma mahaifiyata ta ba shi wasu itama. Wasu mutane sun tuntube ni cewa mu cika masa shagonsa domin dai yanzu babu komai ciki kuma yana zuwa wajen a kullun kwanan duniya kasancewar ya zame masa jiki."

Jama'a sun yi martani

Ter Rā Ph Aboshin ya ce:

"Baba mutumin kirki ne duk sanda na ziyarci bays garden yana kula da ni da kyau.

Agah Samuel ya yi martani:

"Ka yi tunani mai kyau sosai...ka nuna godiya da kuma karamci a lokaci guda."

@John Tumeun ya ce:

"Ya yi kyau. Na san mutumin nan. Ina siyayya wajen shi sosai lokacin da nake yawan zuwa Bays Garden."

A wani labari na daban, wani dalibi mai kwazo da kokarin neman na kai ya mayar da dakin kwanansa na makaranta ya zama wani dan karamin kanti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng