Zaben 2023: Fitaccen Malamin Addini Na Najeriya Ya Bayyana Yan Takarar Shugaban Kasa Da Za Su Fadi Zabe
- Yan takarar shugaban kasa biyu, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, ba za su kai labari ba a zabe, a cewar Fasto Tunde Bakare
- Fasto Bakare ya bayyana hakan ne a baya-bayan nan cikin wata hira; ya kara da cewa mutanen biyu za su iya kai labari da sunyi aiki tare
- Faston na cocin Citadel Global Community ya kara da cewa baya ganin Obi da Kwankwaso za su yi wani tasiri sosai ba tare da hadin kai ba
Babban limamin cocin Citadel Global Community, Fasto Tunde Bakare, bai yi imani cewa Rabiu kwankwaso da Peter Obi za su kai labari ba a zaben shugaban kasa da ke tafe.
Yayin wani hira a baya-bayan nan, Bakare ya ce idan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (Kwankwaso) da na Jam'iyyar Labour (Obi) za su ajiye banbancin siyasa su hada kai, da sunyi tasiri sosai sun jijiga manyan yan takarar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bakare ya ce idan aka yi la'akari da tasirin da Atiku Abubakar da Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, zai yi wahala, su kai ga cimma nasara da takararsu.
Malamin addinin mai karfin fada a ji ya ce:
"Ka yi tunanin idan da Obi da Kwankwaso sun ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu a gefe, suka kafa wata tawaga wacce za ta iya zama madadin wadannan hamshakan masu hannu da shuni, masu gogayya, wadanda suka dade a can, da sun iya girgiza tsarin fiye da yadda suke. yanzu suna yin a matsayin daidaikun mutane suna gudanar da tseren su.
"Da sun girgiza jam’iyyun gaba biyu da sun hada gidajensu amma a yanzu ban ga irin tasirin da za su yi a zaben ba."
Fitaccen faston kudu maso yamma ya juya wa Tinubu baya, ya bada muhimmin dalili
A wani abu da ya yi kama da sako ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progress Congress, APC, Asiwaju Bola Tinubu, Fasto Tunde Bakare, ya ce yan siyasa nagari ba su cewa wasu su amsa tambayoyin da aka musu.
Babban limamin cocin na Citadel Global Community Church (tsohon cocin Latter Rain Assembly) ya furta hakan ne cikin jawabinsa kan batutuwan kasa a ranar Lahadi, 15 ga watan Janairu.
Duk da cewa faston bai ambaci sunan Tinubu ba, ya bada misalai da dama da suka nuna cewa yana nufin dan takarar shugaban kasar na APC ne.
Asali: Legit.ng