Tinubu Na Da Son Mulki irin Na Sarakunan Kama Karya, Yana So Ya Juya Yan Najeriya Kamar Waina, Inji Naja’atu
- Tsohuwar daraktar kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu, Naja’atu Muhammad, ta ce ta bar APC ne saboda dan takarar na APC ba zai iya shugabancin Najeriya ba
- Naja'atu ta yi ikirarin cewa tsohon gwamnan na jihar Lagas kansa kawai ya sani ba Najeriya bace a gabansa
- Tsohuwar sanatan ta bayyana shi a matsayin mutum mai izza wanda ke son juya al'umma da kudin kasar
Abuja - Tsohuwar sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya, Naja’atu Muhammad, ta ce Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), yana da tunani irin na sarakunan kama karya kuma bai damu da kasar ba illa kawai kansa ya sani.
Naja'atu ta bayyana hakan ne lokacin da ta bayyana a wani shiri wanda Arise TV ta watsa a ranar Alhamis, 26 ga watan Janairu.
A kwanan nan ne dai tsohuwar sanatar dai ta fice daga jam'iyyar APC mai mulki a kasar.
Daga bisani aka gano ta tare da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), kuma ta ayyana goyon bayanta gare shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan haka ne kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ta fito ta zarge ta da cin dunduniyar jam'iyyar cewa wannan ne dalilin da yasa aka fatattake ta daga jam'iyyar kafin ta yi murabus.
Na bar APC saboda ganin Tinubu ba zai iya ba, Naja'atu
Da take martani ga furucin APC, Naja'atu ty jaddada cewar ta bar jam'iyyar ne saboda Tinubu ba zai iya ba.
A cewar Naja'atu, Bola Tinubu na neman yadda "zai rike wukar da zai yanka kek" ne da kuma damar iya juya akalar al'ummar Najeriya ta fannin kudi da tunaninsu, rahoton The Cable.
Naja'atu ta ce:
"Na bar APC ne saboda Tinubu ba zai iya ba. Komai a kan Tinubu game da kansa ne. Lokacin da ya so yin takara, ya ce zagayensa ne. Yana so ya rike wukar da za ta iya yanka kek. Ba kasar bane a gabansa sai kansa.
"Lamari ne na son kansa da iko. Ya na son juya kaya da tunanin mutanen kasar nan, musamman yan kudu maso yamma. Na ji shi yana cewa idan ya kwanta bacci, yankin kudu maso gabas na yin bacci. Wannan ne tunaninsa. Tunani irin na sarakunan kama karya."
Atiku na son yaransa 31 su zama attajirai shiyasa yake so ya gaje Buhari, tsohon hadiminsa
A wani labari na daban, tsohon hadimin Atiku Abubakar, Michael Achimugu ya ce tsohon ubangidansa na son zama shugaban kasa ne saboda yaransa su zamo attajirai kamar shi idan kasa ya rufe idanunsa.
Achimugu ya ce yan Najeriya za su tafka babban kuskure idan har suka yarda suka zabi dan takarar shugaban kasar na APC.
Asali: Legit.ng