"Ya Kamata Ku Kusanci Allah", Kwamishinan Yan Sanda Ya Shirya Wa Jami'ansa Musabakar Al-Kur'ani
- Kwamishinan yan sandan Jihar Kebbi ya shirya musabaka ga jami'ansa da nufin kara kusanta su ga Allah
- Manyan malamai sun bawa jami'an shawara akan su sanya koyarwar Qur'ani a rayuwarsu don zamar musu garkuwa gobe kiyama
- Musabakar itace irin ta ta farko tun bayan gina hedikwatar yan sandan Birnin Kebbi a 1991
Jihar Kebbi - Kwamishinan yan sandan Jihar Kebbi, Malam Ahmed Magaji Kontogora ya shirya musabakar Kur'ani ga jami'ansa don kara kusantasu da Allah, rahoton The Sun.
Jami'an da suka shiga musabakar, kimanin su 18, sun fito daga ofisoshin yankuna daban-daban kuma sun fafata a rukuni shida, wanda ya hada da izu 60, izu 40, izu 20, izu 10, izu 5 da kuma izu biyu na Alqur'ani mai girma.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da yake jawabi akan muhimmancin musabakar, kwamishinan yan sandan, Malam Ahmed Magaji Kontogora, wanda shi ya dauki nauyi, ya ce, akwai bukatar jami'an su kara samun kusanci da Allah.
Ya ce:
''Babban dalilin shirya wannan gasar shine don kara cusa tsoron Allah a zukatan jami'an tsaro musamman yan sanda don su gudanar da aikinsu cikin tsoron Allah.
Yayi karin haske cewa dalilin musabakar shine don baiwa jami'an damar samun kariya da kuma kiyayewar Allah lokacin aikinsu.
Da yake bawa jami'an shawara cewa su zama jakadun musulunci na gari, Magaji Kontogora ya roke su da suyi koyi da koyarwar Qur'ani a rayuwarsu ta yau da kullum.
''Kuma muna sa rai, a karshen musabakar da za a karkare cikin kwana uku, wanda suka samu nasara za a basu kyaututtuka da kuma shaida'' ya ce ''wannan musabakar zata taimaka musu su kara sanin mahaliccinsu, ya kuma karfafa musu gwiwa su dinga aiki da koyarwar littafin mai tsarki don tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.''
Sarkin Gwandu ya jinjinawa wadanda suka shirya musabakar
Da yake kaddamar da gasar a babbar hedikwatar yan sanda ta Birnin Kebbi, Sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu-Bashar ya yabawa kokarin wanda suka shirya taron.
Sarkin, wanda ya samu wakilcin babban limamin babban masallacin Birnin Kebbi, Sheikh Muhktar Abdullahi, ya hori jami'an da su zama masu tsoron Allah lokacin gudanar da aikinsu.
A wata huduba mai taken, ''Muhimmancin karanta Qur'ani da kuma aiki da shi'', Sheikh Muhammad Rabi'u-Danjuma ya ce Kur'ani zai zama shaida ga wanda yake yawan karanta shi a gaban Ubangiji a ranar alkiyama a matsayin mai kariya don hana shi shiga wuta.
Rabi'u-Danjuma, wanda akafi sani da Tafawa-Balewa ya hori iyayen yara da su kula da tarbiyar yaransu, yana mai tabbatar da cewa koyawa yara Qur'ani zai sama musu matsayi mai girma ranar Alkiyama.
Da yake karantawa daga cikin Kur'ani da hadisin Manzon Allah (SAW), malamin ya tabbatar da cewa Kur'ani shine babbar hanyar da musulmi zai bi zuwa aljanna.
Ya bada tabbacin:
''Kada matsayinka, dukiya ko ilimin bokonka ya hana ka karanta Kur'ani ko wacce rana. Ba abin da yake wanke zuciya kamar Kur'ani mai tsarki, saboda haka, a karanta Qur'ani iya yadda za a iya saboda zai maka shaida ranar alkiyama."
Tun da fari, shugaban kwamitin shirye-shirye, CSP Aminu Sadiq, ya tabbatar da cewa tun da aka kafa hedikwatar a 1991, ba a taba shirya irin gasar ba sai yanzu.
Asali: Legit.ng