Abun Mamaki: Mabarata a Kaduna Sun ki Karbar Tsohuwar N1,000

Abun Mamaki: Mabarata a Kaduna Sun ki Karbar Tsohuwar N1,000

  • Wasu tarin mabarata da ke bara a titin Kano da ke kwaryar birnin Kaduna, sun ki karbar tsohuwar N1,000 da aka basu sadakar ta
  • Wani matashi mai suna Caleb ya sauka daga bas inda ya bude lalitarsa ya mika musu N1,000 amma mabaratan suka watse
  • Sun koka da cewa koda ya basu basu san inda za su yi da tsohuwar N1,000 illa iyaka ta zama takardar banza a wurinsu

Kaduna - Wasu gungun mabarata da ke fitaccen titin Kano a jihar Kaduna, sun ki karbar N1,000 da wani matashi ya basu sadaka.

Kamar yadda Daily Post ta wallafa a ranar Laraba, mabarata uku ne suka tunkari matashin mai suna Caleb inda suke neman taimako.

Mabarata
Abun Mamaki: Mabarata a Kaduna Sun ki Karbar Tsohuwar N1,000. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Yayin da ya sauka daga bas kuma ya yanke hukuncin baiwa mabaratan tsohuwar takardar N1,000 daga lalitarsa.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

Amma cike da mamaki da ya mamaye shi, mabaratan sun koma baya tare da juyawa suka wuce daga wurinsa inda suka ki karbar kudin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matashin yace:

“Mabaratan sun zo wurina suna neman sadaka. Na basu abinda nake da shi amma suka ki karba.”

Caleb yayi bayanin cewa, duk da kokarin da yayi, tsofaffin kudi kadai ne a jikinsa kuma har yanzu bashi da sababbin da suka fito.

Bankuna na cigaba da bayar da tsofaffin kudi duk da umarnin CBN

A wani labari na daban, bankuna a cikin birnin Kano suna cigaba da fitar da tsofaffi kudi a injinansu na ATM duk da kuwa umarnin da babban bankin Najeriya, CBN ya bayar.

A zagayen da aka yi wasu injinan fitar da kudi na bankuna da dama da ke kwaryar birnin Kano, an ga cewa tsofaffin kudaden N1,000, N500 da N200 ke fita.

Kara karanta wannan

Akwai matsala fa: Direbobi a wata jihar Arewa sun cije, sun fadi abin da suke so CBN ta yi

Jama’a sun koka da rashin yalwatar sababbin kudin a gari duk da kuwa babban bankin Najeriyan ya tabbatar da cewa babu gudu balle ja da baya a wa’adin da suka saka ba mayar da tsofaffin kudi takardun kawai.

Hatta ’yan kasuwa a kasuwar Kantin Kwari da ke kwaryar birnin Kano sun koka kan rashin wadatar wannan sabbin kudin hannun jama’a.

Sun bayyana cewa, ba su ga sabbin kudin da yawa a gari ba duk da sauran kwanaki su daina aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng