Majalisar Dattawa Ta Karrama Malamin Jihar Neja da Yan Ta'adda Suka Kona

Majalisar Dattawa Ta Karrama Malamin Jihar Neja da Yan Ta'adda Suka Kona

  • Majalisar Dattawan Najeriya ta girnama Malamin cocin da yan ta'addan suka kashe a jihar Neja a zamanta na yau Laraba
  • Shugaban majalisar dattawa ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gudsnar da bincike domin cafke masu hannu a hukunta su
  • Bayan nan ne mambobin majalisar su ka yi shiru na minti ɗaya domin karrama mamacin

Abuja - Majalisar dattawa a zamanta na ranar Laraba ta gudanar da shiru na minti ɗaya domin karrama Malamin Coci, Isaac Achi, wanda yan ta'adda suka ƙona har lahira a karamar hukumar Paikoro, jihar Neja.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa har zuwa numfashinsa na ƙarshe, Achi ga kasance shugaban yankin Kiristocin Minna, babban birnin jihar Neja kuma Limamin Cocin St Peter da Paul Catholic dake Kafin Koro.

Majalisar Dattawa.
Majalisar Dattawa Ta Karrama Malamin Jihar Neja da Yan Ta'adda Suka Kona Hoto: NGRsenate
Asali: Facebook

Sanata Sani Musa mai wakiltar gabashin jihar Neja ne ya kawo batun zauren majalisa ya kafa hujja da Oda 42 da 52 domin izinin gabatar da kisan rashin imani da aka yi wa Rabaran Isaac Achi.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Kamfe Saboda Babban Rashi Da Ta Yi A Imo

Daga nan Majalisar dattawa ta miƙa ta'aziyya ga iyalan Mamacin da kuma Bishof na al'ummar kiristocin Minna, sannan mambobi suka yi shiru na minti guda domin girmama Marigayin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban majalisa, Ahmad Lawan ya ce:

"Majalisar dattawa ta yi Allah wadai da kisan Rabaran Isaac Achi tare sauran mutanen da harin ya shafa. Majalisa na kira ga hukumar 'yan sanda sauran hukumomin tsaro da su yi bincike a kama tare da hukunta masu hannu."
"Muna kira ga hukumar ba da agajin gaggauta sake gina gidan Marigayin wanda maharan suka lalata. Muna mika jaje ga Bishof ɗin Minna Diocese, Catholic Faithful da kuma iyalan marigayin."

A rahoton the Nation, bayan wannan jawabin ne majalisar ta yi shiru na Minti ɗaya domin girmama marigayin.

Abinda Muke Yi Domin Kwankwaso Ya Dawo Gida Jam'iyyar PDP, Diri

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda yan Najeriya suka cika bankuna don mayar da tsaffin kudi

A wani labarin kuma Gwamna Diri ya bayyana kokarin da suke na jawo hankalin Kwankwaso ya sauya sheka zuwa PDP

Sanata Rabiu Kwankwaso, mai neman zama shugaban kasa a NNPP ya kai wa Douye Diri ziyara har gidan gwamnati dake Yenagoa.

Gwamna Diri yace shi da wasu manyan siyasa suna ci gaba da Addu'ar wata rana Kwankwaso ya dawo jam'iyyarsa ta asali watau PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262