An Ci Tarar Firaministan Burtaniya Bisa Laifin Rashin Sanya Bel Yayin Tuka Mota
- ‘Yan sanda a kasar Burtaniya sun ci tarar Firaministan kasar bisa karya dokar sanya bel yayin tuka mota a kasar
- Ba wnanan ne karon farko da ake cin tarar shugaba a kasar Burtaniya ba, an yiwa Boris Johnson irin wannan a baya
- Akan samu lokuta da dama a kasashen turai da ake hukunta shugabanni bisa laifin saba rubutacciyar doka
Burtaniya - Rashin sanya bel din mota ya sa an ci tarar Firaiministan Burtaniya, Rishi Sunak, kamar yadda rahotanni suka bayyana, BBC Hausa ta ruwaito.
Wannan ya faru ne bayan da aka ga shugaban na kasar Turai a wani bidiyon da ya dauka a cikin mota ba tare da bel ba.
‘Yan sandan garin Lancashire ne suka yanke masa hukunci ta hanyar sanya masa tara da ba shi wa’adin lokacin da zai biya.
Ya amsa laifinsa, an rubuta masa tara
Da suke bayyana martanin shugaban, sun ce ya amsa laifinsa tare da neman afuwa game da kuskuren da ya aikata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Doka ce a kasa Burtaniya mai kaiwa ga tara idan aka kama mutum yana tuki ba tare da bel ba.
A cewar rahotanni, akan ci tarar mutane a kasar daga fam 100 zuwa wani adadi da dokar ta tanada, rahoton The Guardian.
Amma idan aka je kotu, akan caji wanda ya karya dokar sanya bel kusan fam 500 ko dai adda ta kaya.
Yadda aka kama Firaminista Sunak
Bidiyon da aka ga Sunak ba tare da bel ba ya fito ne daga shafinsa na Instagram, lokacin da ake bayyana kashe-kashen gwamnatin kasar.
Ba kuma wannan ne karon farko da ake cin tarar firaminista a kasar ba, wannan ne karo na biyu da aka hukunta shugaba a Burtaniya.
Idan baku manta ba, a watan Afrilun bara ne aka ci tarar Boris Johnson tara saboda ya karya dokar kulle ta Korona.
A cewar rahoto, ana bukatar mutum ya biya tarar cikin kwanaki 28 ko kuma ya daukaka kara zuwa gaba.
Bayan yanke shawarar daukaka kara, ‘yan sanda ya wajaba su sake duba laifin don duba yiwuwar yafewa ko kuma ci gaba zuwa gaban kotu.
Sunak dai ya zama Firaministan Burtaniya jim kadan bayan da sarauniyar Ingila mai dogon zamani ta kwanta dama.
Asali: Legit.ng