Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Sace Mutane 49 a Jihar Neja

Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Sace Mutane 49 a Jihar Neja

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai mummunan hari a jihar Neja, sun sace amare guda biyu da kuma mutum 47
  • An ruwaito cewa, sun kuma yi awon gaba da kayayyaki masu yawa na mutanen yankin a lokacin harin
  • Ba wannan ne karon farko da 'yan bindiga ke kai hari kan al'ummomin jihar Neja ba, sun sha yin hakan a baya

Jihar Neja - Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun sace mutum 50 a wasu kauyukan da ke jihar Neja, sun yi awon gaba da kayayyakinsu masu daraja.

‘Yan bindigan a barna daban-daban da suka yi a kauyen Kutunku a karamar hukumar Wushishi ta jihar, inda suka sace mutane 19 da suka hada da maza 11 da mata takwas.

Hakazalika, sun kuma kai farmaki a kauyen Jangaru a karamar hukumar Rafi, inda suka sace mutane 30 nan take.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ‘Yan Bindiga Sun Kutsa Kauyen Tafawa Balewa, Sun Halaka Mutum 5 da Sace 1

'Yan bindiga sun yi barna a jihar Neja
Tashin Hankali Yayin Da ’Yan Bindiga Suka Sace Mutane 49 a Jihar Neja | Hoto: newtelegraphng.com
Asali: UGC

An ce ‘yan bindigan sun farmaki wadannan al’ummomin ne da sanyin safiyar yau Litinin 23 ga watan Janairun 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar wani mazaunin yankin da ya tattauna da New Telegraph ta wayar tarho, ‘yan bindigan sun jikkata mutane da yawa yayin wannan barna.

An cewarsa, biyu daga cikin matan da suka sacen aurensu na zuwa nan da karshen makon da ake ciki.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da daliban firamaren gwamnati a jihar Nasarawa

A baya kadan kunji yadda wasu 'yan bindiga suka sace daliban makarantar firamare a jihar Nasarawa da ke kusa da Abuja.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Juma'a daidai lokacin da daliban ke zuwa makaranta da sanyin safiyar ranar, rahoton Vanguard.

Ya zuwa lokacin hada rahoton, hukumomi basu gano adadin daliban da tsagerun suka sace ba, amma an ce ana ci gaba da bincike don gano adadinsu da kwato su.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta, Sun Yi Babbar Ɓarna a Jiha

Wata majiya ta bayyanawa manema labarai yadda lamarin ya faru, kana rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin.

An kashe jami'an tsaro, ana neman masu maye gurbinsu

A wani labarin kuma, 'yan bindiga sun hallaka wasu jami'an tsaron NSCDC a jihar Kaduna, rundunar ta ba da gurbin maye su.

An ba danginsu kudade tare da basu hakurin rashin ahalinsu yayin wata ziyara da hukumar ta kai.

Ana yawan samun lokutan da 'yan ta'adda ke hallaka jami'an tsaron Najeriya da ke bakin aiki a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.