Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane Shida a Jihar Enugu

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane Shida a Jihar Enugu

  • Miyagun yan bindigan da ba'a san su ba sun yi awon gaba da mutane shida a jihar Enugu jiya Asabar
  • Bayanai daga bakin wani shugaban al'umma sun nuna cewa maharan sun zo da manyan makamai suka bude wuta
  • Har yanzun hukumar yan sandan jihar ba tace uffan ba kan abinda ya faru kuma maharan ba su kira iyalai ba

Enugu - Wasu miyagun 'yan bindiga sun yi awon gaba da mutane Shida cikinsu har da matashi mai yi wa kasa hidima a kauyen Ikem, karamar hukumar Isi-Uzo, jihar Enugu.

Yankin ƙaramar hukumar na fama da yawan hare-hare a 'yan makonnin nan bayan zargin da ake cewa mayakan Fulani sun nemi mafaka a Eha-Amufu.

Harin yan bindiga.
Miyagun 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane Shida a Jihar Enugu Hoto: leadership
Asali: Twitter

Wani ganau kuma shugaban wata ƙungiya mai son kawo ci gaba reshen jihar Enugu, Emeka Odoh, ya ce tsawon kwana uku 'yan bindigan masu rufe fuskokinsu suka kwashe suna addabar mutane.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Hedkwatar 'Yan Sanda, Sun Ta Da Bama-Bamai

Yace maharan sun kai faramki Ikem-Isioroto da ke kan Titin Obollo Afor – Nkalagu, sannan suka iza keyar mutanen zuwa cikin daji, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Odoh ya ce ya dawo gida ne daga Enugu domin haɗa karfi da sauran mutanen garin su nemo hanyar kara inganta tsaro gabanin babban zabe domin ta haka ne kaɗai mutane zasu jefa kuri'unsu cikin kwanciyar hankali.

A kalamansa ya ce:

"Lokacin da muka bar ɗakin taron kowa zai koma gida sai muka ga 'yan bindiga su hudu kan Titin, ina tuki na yi hanzarin jan motar baya ashe akwai wani rukunin 'yan bindiga a bayan mu."
"Nan fa suka bude mana wuta suna farfasa gilasan motar da Tayoyi hudu, amma haka na ci gaba da tuƙa motar domin tsira da rayuwarmu. Ɗaya daga cikin mu harsashi ya same shi, aka yi saurin kai shi Asibiti a Enugu.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Nemo Magani, Ya Bayyana Yadda 'Yan Najeriya Zasu Kawo Karshen Yan Bindiga

"Sai da Likitoci suka cire harsasai 8 a jikinsa, har yanzu yana sashin kula na Asibitin yana samun sauki."

Mista Odoh ya kara da cewa har yanzu maharan ba su nemi iyalan wadanda suka sace don neman kudin fansa ba.

Rundunar yan sanda reshen jihar Enugu ba tace komai ba kan harin har zuwa lokacin haɗa masu rahoton nan wanda Channels tv ta tabbatar.

An kaiwa ayarin ɗan takarar gwamna hari a Ribas

A wani labarin kuma Miyagu Sun Farmaki Dan Takarar Gwamna a Jihar Ribas, Sun Tafka Barna

Rahotanni daga jihar Ribas sun tabbatar da cewa wasu yan baranda sun bude wa ayarin ɗan takarar gwamna wuta a jihar Rabas ranar Asabar da ta gabata.

Ɗan takaran wanda ya tsira daga harin, ya nuna danuwarsa kan yadda siyasar Ribas ke sauya akala zuwa ta zubda jini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel