Wannan Ba Almubazaranci Bane? Bidiyon Dankareren Gidan Dino Melaye a Kogi Ya Haddasa Cece-kuce

Wannan Ba Almubazaranci Bane? Bidiyon Dankareren Gidan Dino Melaye a Kogi Ya Haddasa Cece-kuce

  • Jama'a a soshiyal sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da bidiyon hadadden gida mallakin Sanata Dino Melaye
  • Dino ya kera dankararen gina wanda ya amsa sunansa aljannar duniya a mahaifarsa ta Aiyetoro Gbede, jihar Kogi
  • Wasu na ganin hakan a matsayin almubazaranci domin a cewarsu kudin kula da gidan don kada ya lalace zai ci akalla N200m

Sanata Dino Melaye ya kasance dan siyasa mai son jin dadin rayuwa da nuna ki kuma sau da dama ya sha wallafa gidaje, motoci da ababen more rayuwa da ya mallaka a soshiyal midiya.

A wata wallafa da ya yi a Facebook, tsohon sanatan na Kogi ya wallafa bidiyon katafaren gidansa da ke mahaifarsa a Aiyetoro Gbede, jihar Kogi.

Katafaren gida da Dino Melaye
Wannan Ba Almubazaranci Bane? Bidiyon Dankareren Gidan Dino Melaye a Kogi Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: Dino Melaye
Asali: Facebook

A wani bidiyo da Legit.ng ta gani, an jiyo muryan wani mutum yana nuna manyan gine-ginen da ke cikin wannan katafaren gida.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Ganduje Ta Jawo Farfesa Jega, Ta Hada Shi da Wani Babban Nauyi a Najeriya

"Wannan shine gidan Sanata Melaye a mahaifarsa da ke Aiyetoro Gbede a karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi," cewar muryar a bidiyon yayin da ya fara haska koina na gidan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ainahin ginin gidan da masaukin baki

Wanda ke daukar bidiyon gidan ya hasko ainahin katafaren ginin gidan da kuma masaukin baki mai dakuna shida wadanda aka yiwa fenti fari.

"Katafaren gida ne mai girma sosai kuma yana da yalwataccen fili," cewar mai jawabin yayin da yake ciki gaba da hasko wurare daban-daban na ginin gidan.
"Akwai filin buga kwallo tsakanin ainahin gidan da masaukin baki."

A cewar mai jawabin, masaukin bakin kadai yana da dakunan bacci guda shida a cikinsa.

"Kuna iya ganin gidan, katafaren gida, katafaren harabar gida," mai jawabin na ta nanatawa yayin da yake ci gaba da nuna bangare-bangare na gidan.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Aka Tsinci Gawar Farfesan Najeriya Da Mace A Cikin Gida A Amurka

Sashin wasanni da majami'a inda Melaye ke bauta

Bayan masaukin bakin akwai wani babban filin wasa, mai matukar girma. Wajen buga kwallon tebur da kuma kwallon raga.

Hakazalika a cikin gidan akwai wani babban mujami'a, a cewar mai jawabin, jigon na PDP ya gina shi ne bayan mutuwar mahaifiyarsa, Deaconess Comfort Melaye.

Sanata Melaye na bauta a cikin mujami'ar duk sanda ya je kauyen, inji mai jawabin.

Abun da yan Najeriya ke fadi

Da yake martani kan bidiyon da aka wallafa a Facebook, Ehinmola Oluwatomisin Olawumi Justus ya ce:

"Wannan ya yi kyau, kasancewar a mahaifarka ka gina wannan ya kara maka kima a idona, Allah ya albarkaceka ga al'ummarka."

Aderemi Adeeko ya ce:

"Katafaren gida da bangarori da dama da sauransu."

Eric Dibia ya ce:

"SDM, wannan almubazaranci da dukiya ne, kana zuwa Aiyetoro Gbede ne lokaci zuwa lokaci sannan kana zama a Abuja da kum yawo a duniya, idan za ka gyara gidan nan sai ka kashe kusan 200m ko fiye da haka, wannan ba almubazaranci bane?"

Kara karanta wannan

Babu Ruwanmu da NEPA: Budurwa Ta Nunawa Duniya Katafaren Gidan Iyayenta a Bidiyo, Jama'a Sun Shiga Mamaki

Matashi ya kama kifi mai launin ruwan gwal, ya nemi shawarar jama'a

A wani labarin kuma, wani matashi ya bazama neman shawarar jama'a a soshiyal midiya bayan ya kama wani kifi mai launin ruwan gwal.

Mutumin ya nemi sanin daraja da kuma sunan kifin don kada ya lamushe abun da ka iya zama tushen arzikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel