Ba a Gama da Cece-Kucen Sabbin Naira Na Wankewa Ba, an Gano Rashin Daidaito a Bugunsu

Ba a Gama da Cece-Kucen Sabbin Naira Na Wankewa Ba, an Gano Rashin Daidaito a Bugunsu

  • 'Yan Najeriya a kafar Twitter sun shiga mamaki bayan gano yadda aka buga sabbin Naira da kura-kurai
  • Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan da sabbin kudaden suka fara yawo a kasar tare da jiran karshen tsoffi
  • A baya 'yan Najeriya sun shiga damuwar yadda kudaden ke wankewa idan sun gamu da ruwa ko wani abu danye

Najeriya - Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kuka da nuna damuwa game da launi da kargon sabbin Naira da aka buga, sun kara gano wasu matsalolin da suka jawo cece-kuce a Twitter.

A wasu hotunan da aka yada na sabbin N500 da N1,000, an ga yadda aka samu tsaiko wajen bugawa da yanka su.

A jikin wata N500, an ga yadda bugun ya yanke daga jikin wani, lamarin da yasa kudin ya zama mai kama da rabi-da-rabi.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Majalisa za ta kawo mafita, ta fadi abu na farko da za ta yi

Yadda sabbin Naira suka zo da matsala
Tashin Hankali Ga Su Buhari, Shugaban Yakin Kamfen Bola Tinubu Ya Fice Daga APC | Hoto: @ComrHaroun
Asali: Twitter

A bangaren N1,000 da muka gani, akwai dan daurin takarda da aka yanka tare da kudin, inda ya zamewa takardar kudin kamar wani dan 'kari' ne na kuskure da rashin kula wajen aikin buga kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da Legit.ng Hausa ta duba kafar Twitter, ta ga yadda mutane da yawa na ta maganganu tare da bayyana alhini ga wannan lamari da ya shafi kudin kasa masu daraja.

Kalli hotunan:

Martanin jama'a

Mun tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa, kamar dai haka:

@SavvyRinu

"Halin ko-in-kula irin na Najeriya ne."

@CPaul126

"A'a, suna bugawa da injunan bugu daban-daban.Wasu suna da launi mai dubu wasu kuma haske. Wasu suna kodewa. Wasu za asu yage idan suka taba ruwa..."

@owesley17

"N1,010, dole wancan karin a kirga shi a matsayin wani abu fa."

@iamspotlex

"Yi amfani da almakashi ✂️ ka daidaita shi, injin bugu da saiti na CBN sun gama lalacewa ne."

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: CBN ya kawo mafita ga mutanen kauye, ya kawo wani sabon tsari mai kyau

@Frankeelodeo

"Har tsoffin kudin ma magana ta gaskiya suna da irin wannan illar."

Launi kadai aka sauya, 'yan Najeriya sun yi martani ga zubin sabbin Naira

A wani labarin kuma, kun ji yadda 'yan Najeriya ke nuna damuwa da dasa alamar tambaya game da sabbin Naira.

A kafar sada zumunta, an yada bidiyon yadda kudin ke wankewa su koma farar takarda saboda rashin kargon bugu.

Mun tattaro muku martanin jama'a game da wannan lamari, sun ce launi kadai aka sauyawa kudin Naira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel