Ministan Harkokin Kasashen Waje Na Gabon Ya Rasu Ana Gab da Shiga Taro

Ministan Harkokin Kasashen Waje Na Gabon Ya Rasu Ana Gab da Shiga Taro

  • Allah ya yi wa ministan harkokin waje na kasar Gabon, Moussa Adamo, rasuwa sakamakon bugawar zuciya
  • Bayanai sun nuna cewa marigayin na zaune yana dakon fara taron majalisar ministoci ranar Jumu'a kwatsam abun ya faru
  • Shugaban kasa Bango ya bayyana mutuwar ministan da wani babban rashi da ƙasar Gabon

Gabon - Ministan harkokin kasashen waje na kasar Gabon, Michael Moussa Adamo, ya rasu ranar Jumu'a sakamakon bugawar zuciya yayin da yake jiran shiga taron majalisar zartaswa.

A wata gajeruwar sanarwa da gwamnatin Gabon ta fitar ta bayyana cewa Moussa Adamo, ɗan shekara 62 ya rasu bayan fama da bugun zuciya duk da kokarin kwararrun Likitoci na ceto shi.

Michael Moussa Adamo.
Ministan Harkokin Kasashen Waje Na Gabon Ya Rasu Ana Gab da Shiga Taro Hoto: vanguardngr
Asali: UGC
"Ya zauna a ɗakin jira mintuna kaɗan gabanin fara taron majalisar ministoci, a gaban wasu daga cikin abokan aikinsa a gwamnati ya fara jin alamun rashin lafiya."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Ganduje Ta Jawo Farfesa Jega, Ta Hada Shi da Wani Babban Nauyi a Najeriya

Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta tace an yi hanzarin kai Ministan Asbitin Sojoji yayin da abun ya tsananta amma rai ya yi halinsu da tsakar rana.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan babban rashi ne ga ƙasar Gabon

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa da yake martani kan lamarin, shugaban ƙasa Bango ya ayyana marigayi Moussa Adamo a matsayin abokin hulda kuma dattijon ƙasa.

"Tun fari ya kasance aboki, mai biyayya da yakini, wanda a ko da yaushe nake lissafa shi a sahun farko. Wannan ba karamin rashi bane ga kasar Gabon," inji shugaban kasa.

Waye marigayi Moussa Adamo?

An haifi Moussa Adamo a garin Makokou dake arewa maso gabashin Gabon a shekarar 1961 kuma ya fara aiki ne a matsayin mai gabatarwa a gidan Talabijin.

A 2000, aka naɗa shi shugaban ma'aikata ga Ministan tsaro, wanda a wancan lokacin shi ne Bango, shugaban kasa mai ci a yanzu.

Kara karanta wannan

Kamfen zub da jini: An sheke wani, da dama sun jikkata a kamfen PDP a wata jihar APC

Lokacin da aka zabi Bango a matsayin shugaban kasa bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo Ondimba, a 2009, Moussa Adamo ya koma matsayin mashawarci na musamman.

Bayan shekaru 10 a matsayin Ambasadan Gabon a kasar Amurka zuwa 2020, ya zama Ministan tsaro daga baya kuma ya koma Ministan harkokin waje a watan Maris na bara.

A wani labarin na daban kuma Matar da Tafi Kowa Tsufa a Duniya ta Mutu a Birnin Toulon

Sister Andre mai asalin suna Lucile Randon 'yar asalin kasar Faransa ita ce 'dan Adama mafi tsufa a yanzu a duniya, kuma ta mutu tana da shekaru 118.

Ta kafa tarihin zama mutum mafi tsufa a duniya da ta taba kamuwa da cutar korona a 2021 kuma ta warke sarai, wanda littafin Guinness ya shaida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262