'Diyar Ganduje Ta Ce Zata Mayar Da Kudin Sadaki N50,000 ga Mijinta a Raba su
- Ana cigaba da zaman shari'a tsakanin Hajiya Asiya Ganduje da mijinta Alhaji Inuwa Uba a jihar Kano
- Asiya Ganduje na bukatar kotu ta raba aurenta da Uba Inuwa saboda wasu dalilai na ta
- Shi kuwa mijin ya kindaya wasu sharruda da ya wajaba ta cika masa kafin ya amince a raba auren
Kano - Asiya Ganduje, diyar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ta sake jaddadawa kotu bukatar a raba aurenta na tsawon shekaru 16 da Alhaji Inuwa Uba.
Asiya, a ranar Alhamis ta bayyanawa kotun Shari'ar Musulunci dake Kano cewa shirye take ta mayarwa mijin da N50,000 kudin sadakin da ya biya kanta.
Ta bayyana cewa tana neman khul'i a kotun ne saboda ta gaji da zama da mijinta Inuwa kuma a kawo karshen auren, rahoton Vanguard.

Asali: Facebook
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A zaman ranar Alhamis, lauyan Asiya, Ibrahim Aliyu-Nassarawa, ya laburtawa kotu cewa shirya Asiya take da mayarwa mijin kudin sadakin da ya biya N50,000 kanta don ya sake ta.
Yace:
"Kowace mace dake zaman gidan auren da bata jin dadi na da hakki karkashin shari'ar Musulunci ta garzaya kotu neman a raba auren da sharadin za ta mayar da kudin sadaki."
"Wacce nike tsayawa shirye take ta mayar da N50,000 da mijin ya biya sadaki don a raba auren."
Ibrahim Aliyu-Nassarawa ya kara da cewa ta shirya hakuri da dukkan wani hakki na ta amma dai ba zata bi sharrudan da mijin ke kokarin kakaba mata ba, rahoton ya kara.
A cewarsa:
"Sharrudan da ya gindaya abu ne na rikici saboda haka ya kamata ayi zama na musamman a wani kotun."
Shi kuwa lauyan mijin, Umar I. Umar, ya ce matsalarsu ba kudin sadakin N50,000 bane.
A cewarsa:
"Wanda nike wakilta na da sharruda biyu game da wasu dukiyoyinsa, kafin a zo maganasr rabuwar aure."
"Akwai 'yaya hudu da ta haifa masa amma duk yunkurin sulhun da aka yi ya ci tura."
"Idan tana son a raba auren ta dawo da dukkan takardunsa, takardun gidajensa, motoci, da hannun jarin da take da shi a kamfanin shinkafarsu."
Alkali mai shari'a, Malam Halliru Abdullahi, bayan sauraron jawabansu ya dake zaman zuwa ranar 2 ga watan Febrairu, 2023 don yanke hukunci.
Asali: Legit.ng